Buhari mashirmanci ne, yana yaro lokacin da muka kwatowa Najeriya yanci, Ayo Adebanjo

Buhari mashirmanci ne, yana yaro lokacin da muka kwatowa Najeriya yanci, Ayo Adebanjo

  • Shugaban kungiyar Yarabawa ya caccaki jawabin da Buhari yayi ranar Juma'a
  • Buhari ya bayyana cewa ko ta kaka Najeriya ba zata rabu ba
  • Ayo Adebanjo yace Buhari ya koma ya karanci tarihi saboda yaro ne lokacin da sukayi fafutuka

Shugaban kungiyar Afenifere, Cif Ayo Adebanjo, ya caccaki Shugaban kasa Muhammadu Buhari, kan jawabin da yayi ranar 1 ga watan Oktoba ga yan kasa cewa Najeriya ba zata taba rabuwa ba.

Adebanjo ya ce ya kamata ace Buhari mai shekaru 78 da haihuwa ya fahimci cewa tattaunawa da yarjejeniya akayi kafin aka samu yancin kai a 1960.

A hirar da yayi da Jaridar Punch ranar Juma'a, Adebanjo yace kodayake Buhari yaro ne a lokacin, bai san abinda ya faru ba.

Adebanjo wanda shekarunsa 93 yanzu ya kara da cewa irin wadannan kalamai na Buhari ke tayar da tarzoma.

Read also

Da dumi: Yan majalisa sun kalubalanci Buhari ya bayyana sunan wanda ke daukan nauyin Kanu da Igboho cikinsu

Zaku tuna cewa a ranar Juma'a, Buhari yayi jawabi ga yan Najeriya don murnar shekaru 61 da samun yanci.

Adebanjo yace a shekarar 1953, yan Arewa ne suka fara watsi da lamarin samun yancin kai inda suka ce 'A raba Najeriya'.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewarsa, Cif Obafemi Awolowo da Nnamdi Azikwe ne suka janyo hankalin Ahmadu Bello cewa gwanda a zauna tare a samun yancin kai daga Turawan mulkin mallaka.

Adebanjo yace:

"Shi (Buhari) shirme yake fadi. Ire-iren wadannan maganganu ke tayar da rikici. Ta yaya Shugaban kasan al'umma daban-daban, masu yare daban-daban, yace ba za'a iya tattauna rabuwar Najeriya ba? Mun tattauna lamarin rabuwar kai a 1954 kafin samun yancin kai."
"Tattaunawar da mukayi a taron gangamin Landan ne ya haifar da kundin tsarin mulkin 1960."
"Amma ba zan ga laifinsa ba. Yana makaranta firamare lokacin, saboda haka ba zai fahimta ba. Ya koma ya karanta tarihi."

Read also

Rahoto: Yadda Bagudu ya wawuri biliyoyi tare da boyesu a ketare tun zamanin Abacha

Buhari mashirmanci ne, yana yaro lokacin da muka kwatowa Najeriya yanci, Ayo Adebanjo
Buhari mashirmanci ne, yana yaro lokacin da muka kwatowa Najeriya yanci, Ayo Adebanjo
Source: Twitter

Bankin duniya ya ja kunnen Najeriya kan ta guji kashe kudi mara amfani

Bankin duniya ya shawarci Najeriya da sauran manyan kasuwanni da su datse kashe kudi mara amfani kuma su nemi gyararren tsarin bashi domin inganta tattalin arzikin jama'arsu.

Shugaban bankin, David Malpass, ya yi kira ga duniya kan hadin kai wanda ya hada da bangarori masu zaman kansu wurin samar da bashi ga kasashen duniya masu fama talauci, The Nation ta wallafa.

Source: Legit

Online view pixel