Bankin duniya ya ja kunnen Najeriya kan ta guji kashe kudi mara amfani

Bankin duniya ya ja kunnen Najeriya kan ta guji kashe kudi mara amfani

  • Bankin duniya ya shawarci kasar Najeriya da ta datse kisan kudin da ta ke yi mara amfani
  • David Malpass, shugaban bankin, ya shawarci Najeriya da ta nemi gyararren tsarin bashi
  • Malpass ya ce talakawa kawai a ke bari da wahala inda talauci da rashin kiwon lafiya ke yawaita

Kartoum, Sudan - Bankin duniya ya shawarci Najeriya da sauran manyan kasuwanni da su datse kashe kudi mara amfani kuma su nemi gyararren tsarin bashi domin inganta tattalin arzikin jama'arsu.

Shugaban bankin, David Malpass, ya yi kira ga duniya kan hadin kai wanda ya hada da bangarori masu zaman kansu wurin samar da bashi ga kasashen duniya masu fama talauci, The Nation ta wallafa.

Bankin duniya ya ja kunnen Najeriya kan ta guji kashe kudi mara amfani
Bankin duniya ya ja kunnen Najeriya kan ta guji kashe kudi mara amfani. Hoto daga thenationonlineng.net
Asali: UGC

The Nation ta ruwaito cewa, yayin jawabi a Khartoum da ke kasar Sudan, Malpass ya ce juyawa na barazana ga rayukan jama'a, ayyuka, tsarin rayuwa da kuma juriya.

Kara karanta wannan

'Yan fashi sun afka wa coci domin sace kudi, sun daba wa mai gadi wuka a Abuja

"A wurare da yawa na duniya, talauci na karuwa, yanayin rayuwa mai kyau da kuma jahilci na hauhawa, daidaikon jinsi, abinci mai kyau da kiwon lafiya mai kyau suna raguwa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Ga wasu kasashen, ba su iya daukan nauyin basukansu kafin rikicin kuma yanzu cigaba ya ke. A maimakon karuwa, talakawa ne a ka bari a baya suna shan wahala. Wannan sauyin da tattalin arziki ke samu da rashin cigaba shi ke samar da matsala a tattalin arziki, siyasa da alakar yankuna."

Kashe-kashe: A bayyane ya ke, yaƙar jama'ar mu ake yi, Gwamnonin Kudu maso gabas

A wani labari na daban, Gwamnan jihar Ebonyi kuma shugaban kungiyar gwamnonin kudu maso gabas, Dave Umahi, ya ce sun gano cewa an kaddamar da yaki kan yankinsu a yayin da ya ke martani kan kashe-kashen da 'yan bindiga ke wa jama'arsu.

Kara karanta wannan

Shekarau ya ba Gwamnonin jihohin Kudu shawara, yace su daina barazana kan batun 2023

Kamar yadda Leadership ta ruwaito, Gwamna Umahi ya nuna damuwarsa da alhini kan kisan rayuka 12 da aka yi a yankin a makon da ya gabata kuma ya ce babu gaira balle dalili.

Gwamnan ya sanar da hakan ne yayin taron majalisar tsaro na jihar a ofishin sabon gwamnan Abakaliki. Ya zargi wasu Ndigbo da ke zama a kasashen ketare da shirya rigingimun tare da daukar nauyinsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng