Da dumi: Yan majalisa sun kalubalanci Buhari ya bayyana sunan wanda ke daukan nauyin Kanu da Igboho cikinsu

Da dumi: Yan majalisa sun kalubalanci Buhari ya bayyana sunan wanda ke daukan nauyin Kanu da Igboho cikinsu

  • Yan Majalisa sun yiwa Shugaba Muhammadu Buhari raddi kan zargin da yayi musu
  • Shugaba Buhari ya zargi daya daga cikinsu da daukar nauyin yan tawaye
  • Shugaban kasan zai gurfana gaban yan majalisan ranar Alhamis

Abuja - Yan majalisar wakilan tarayya sun kalubalanci Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana sunan dan majalisan da yace shi ke daukan nauyin Sunday Igboho da Nnamdi Kanu.

A cewar TVC, yan majalisan sun bayyana hakan ne a zaman majalisar yau Talata, 5 ga Oktoba, 2021.

Da dumi: Yan majalisa sun kalubalanci Buhari ya bayyana sunan wanda ke daukan nauyin Kanu da Igboho cikinsu
Da dumi: Yan majalisa sun kalubalanci Buhari ya bayyana sunan wanda ke daukan nauyin Kanu da Igboho cikinsu
Asali: UGC

Dan majalisar tarayya ke daukar nauyin Sunday Igboho da Nnamdi Kanu, Buhari ya yi ikirari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi ikirarin cewa wani dan majalisar tarayya ne ke da alhakin daukar nauyin masu kira-kirayen neman ballewar kasar nan.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Shugaba Buhari ya yi ganawar sirri da Goodluck Jonathan

Shugaban kasar ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi ga kasar a matsayin wani bangare na bikin ranar 'yancin kai.

Ya bayyana cewa an gano hakan ne yayin da ake gudanar da bincike bayan kamun Nnamdi Kanu, shugaban masu fafutukar neman kasar Biyafara da kuma Sunday Igboho, shugaban masu fafutukar kasar Yarbawa.

Shugaba Buhari zai gabatar da kasafin kudin 2022 a ranar Alhamis ga majalisar dokoki

Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai gabatar da daftarin kasafin kudin shekarar 2022 ga hadin gwiwar majalisar dokokin kasar a ranar Alhamis mai zuwa, Vanguard ta ruwaito.

Mataimakin shugaban majalisar dattijai, Ovie Omo-Agege ne ya bayyana hakan a ranar Talata 5 ga watan Oktoba a zauren majalisar dattawa da ke Abuja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng