Benue: 'Yan bindiga sun halaka rayuka 2 a sabon farmaki

Benue: 'Yan bindiga sun halaka rayuka 2 a sabon farmaki

  • Gagararrun 'yan bindiga a ranar Alhamis sun zagaye yankin Nyiev da ke karamar hukumar Guma ta jihar Benue
  • A wannan farmakin ne miyagun suka sheke rayuka biyu bayan bude wa mazauna yankin wuta da suka yi
  • Mazauna yankin sun ce 'yan bindigan da suka kai farmakin masu kutse ne a gonakin kauyen wadanda suka addabe su

Guma, Benue - Miyagun 'yan bindiga sun halaka rayuka biyu a yankin Nyiev da ke karamar hukumar Guma ta jihar Benue.

Lamarin ya faru ne kusan kwana biyu bayan da aka kashe rayuka tara a wurare daban-daban na karamar hukumar, Daily Trust ta wallafa.

Benue: 'Yan bindiga sun halaka rayuka 2 a sabon farmaki
Benue: 'Yan bindiga sun halaka rayuka 2 a sabon farmaki. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Shugaban karamar hukumar Guma ta jihar Benue, Caleb Aba, ya sanar da Daily Trust cewa, a ranar Alhamis 'yan bindigan suka zagaye yankin Nyiev kuma suka bude wa mazauna yankin wuta.

Kara karanta wannan

Boko Haram sun gurgunta mulki a Neja, sun kayyade shekarun aurar da 'ya'ya mata

Ya ce 'yan bindigan tsageru ne da suka kutsa gonakin kayukan yankin a ranar Laraba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce sun kai wa hukumomin tsaro korafi kuma suna iyakar kokarinsu wurin ganin sun dakile sake kai farmakin.

A yayin da aka tuntubi mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar Benue, DSP Catherine Anene ta ce ba ta samu labarin aukuwar lamarin ba har yanzu.

El-Rufai: Sakarci ne ka kalmashe a Legas ko Fatakwal kana son a miko muku mulki

A wani labari na daban, Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya yi karin haske kan matsayar kungiyar gwamnonin arewa kan mika mulki kudancin Najeriya, Daily Trust ta ruwaito hakan.

A wani taro a Kaduna a ranar Litinin, gwamnonin sun ce mulkin karba-karba na shugabancin kasa ba ya daga cikin kundin tsarin mulkin Najeriya.

Kara karanta wannan

Ta fashe: Sirrin kazamar dukiyar shugabannin duniya 35, 'yan siyasa 330 da biloniyoyi 130 a kasashe 91

Sun sanar da hakan ne yayin martani ga bukatar takwarorinsu na kudu wanda suka bukaci yankinsu ya samar da shugaban kasa a nan gaba.

A zantawar da yayi da manema labarai, El-Rufai ya ce kada wanda yayi tsammanin cewa zai iya kalmashe kafafu a Legas ko Fatakwal kuma ya yanke hukuncin abinda ya dace arewa ta yi ko wa ya dace 'yan arewa su zaba.

Ya ce in har kudu na son mulki, toh ta shirya tattaunawa da arewa tare da sasanci har a fitar da wanda ya dace a zaba, ba wai a nemi saka wa arewa yin abu dole ba.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel