2023: Ku zo mu hada kai da juna maimakon rikici da juna, Ganduje ya yi kira ga Gwamnonin Kudu
- Gwamnonin Arewacin Najeriya da na kudancinta sun samya kafar wando daya
- Gwamnonin sun yi hannun riga kan lamarin wanda zai gaji Buhari a 2023
- Gwamnan Kano ya yi kira da gwamnoni su hada kai da juna
Kano - Gwamnan Jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya bukaci Gwamnonin Kudanci da Arewacin Najeriya da suyi watsi da sabanin dake tsakanin su domin su cigaba da zama tsintsiya Madaurin ki daya don ciyar da Kasar gaba.
Gwamnan yayi wannan Kiran ne lokacin da yake jawabi wajen bikin Cikar Najeriya shekaru 61 da samun yancin kai a Sani Abacha Stadium dake Kofar Mata.
Hadimin daukar hotunan Ganduje, Aminu Dahiru, ya bayyana a shafin gwamnan na Facebook.
Ya kara da cewa gwamnan ya kuma yabawa jami'an tsaro bisa aiki da suke ba dare ba rana wajen tabbatar da tsaro a fadin Jihar Kano inda yace Gwamnatin sa zata cigaba da nemo hanyoyi na zamani domin tabbatar da tsaron lafiya da dukiyoyin al'umma.
Taron ya sami halartar mataimakin Gwamna, Dr. Nasiru Yusuf Gawuna da Sarakunan Kano masu daraja ta daya da shugabannin hukumomin tsaro da yan majalisu da shugabannin yan kasuwa da kuma daukacin Jami'an Gwamnati.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Baku isa ku tilasta mana mu baku shugabancin Najeriya ba, El-Rufa'i ya fadawa Gwamnonin Kudu
Shi kuwa, Gwamnan Kaduna, Malam Nasiru El-Rufa'i, yace gwamnonin kudu ba zasu tilastawa Arewa ta miƙa shugabancin Najeriya ga yankinsu ba.
El-Rufa'i ya faɗi haka ne yayin da yake tsokaci kan bukatar gwamnonin kudu cewa yankinsu ne zai fitar da shugaban ƙasa da zai gaji Buhari.
Malam Nasiru, wanda ya bada shawarar baiwa kudanci shugaban ƙasa, yace gwamnonin kudu sun ɗauki abun da zafi, da har zasu ce wajibi a ba su shugaban ƙasa a 2023.
Yace:
"Ba zaku tilasta mana sai mun baku shugaban ƙasa ba, amfani da kalmar 'Ɗole' na nufin ko muna so ko bamu so, meyasa zaku kawo batun wajibi a harkokin siyasa?"
"Babu wani abu mulkin karba-karba a kundin tsarin mulki, waɗannan abubuwan ana yinsu ne domin haɗin kai da sulhu."
Asali: Legit.ng