Shugaba Muhammadu Buhari ya dira birnin Addis Ababa halartan bikin ranstarwa

Shugaba Muhammadu Buhari ya dira birnin Addis Ababa halartan bikin ranstarwa

  • Buhari ya isa kasar Habasha da daren Lahadi
  • Wannan ya biyo bayan killace kansa na mako daya da yayi
  • Buhari zai dawo Najeriya ranar Talata

Shugaba Muhammadu Buhari ya dira Addis Ababa, babbar birnin kasar Habasha yau Asabar, 3 ga Oktoba, 2021 domin halartar bikin rantsar da Firai Minista, Abiy Ahmed, karo na biyu.

Fadar Shugaban kasa ta saki hotunan Shugaba Buhari tare da Firai Ministan, Shugaban kasar Habasha, Sahle-Work Zewde da Shugaban kasar Senegal, Macku Sall.

An shirya yin bikin gobe Litinin, 4 ga Oktoba.

Shugaba Buhari ya dira birnin Addis Ababa halartan bikin ranstarwa
Shugaba Muhammadu Buhari ya dira birnin Addis Ababa halartan bikin ranstarwa Hoto: Buhari Sallau
Source: Facebook

Shugaba Muhammadu Buhari ya dira birnin Addis Ababa halartan bikin ranstarwa
Shugaba Muhammadu Buhari ya dira birnin Addis Ababa halartan bikin ranstarwa Hoto: BUhari Sallau
Source: Facebook

Read also

Da duminsa: Majalisar dattarwa ta tabbatar da sunaye 5 da Buhari ya aike mata a matsayin mambobin hukumar EFCC

Shugaba Buhari ya dira birnin Addis Ababa halartan bikin ranstarwa
Shugaba Muhammadu Buhari ya dira birnin Addis Ababa halartan bikin ranstarwa Hoto: BUhari Sallau
Source: Facebook

Shugaba Buhari zai tafi kasar Habasha domin halartan biki

Mun kawo muku cewa bayan mako daya da dawowarsa daga kasar Amurka, shugaba Buhari ya kudirci niyyar sake shillawa kasar Habasha ranar Lahadi.

Daga cikin wadanda zasu yiwa Buhari rakiya akwai ministan harkokin waje Geoffery Onyeama da Shugaban Hukumar Leƙen Asiri ta NIA, Ambasada Ahmed Rufai Abubakar.

Tuni da shugaba Buhari ya aike sakon taya murna da Firai Ministan inda ya tabbatar masa da goyon bayan Najeriya.

Buhari yace:

"A madadin ya Najeriya, ina mika sakon taya murnata ga al'ummar Habasha bisa kokarinku wajen zabe kuma ina kira gareka ka cigaba da ayyukan kwarai ga al'ummarka."

Source: Legit Nigeria

Online view pixel