NAFDAC ta kama mutane 24 da ke sayar da maganin ƙarfin maza a Sokoto

NAFDAC ta kama mutane 24 da ke sayar da maganin ƙarfin maza a Sokoto

  • An kama masu sayar da magungunan karfin maza marasa rajista a jihar Sokoto
  • NAFDAC ta ce kayan da aka kama a birnin Sokoto da kasuwa sun kai na Naira miliyan 2
  • An gargadi mutane su guji shan magunguna marasa rajista da ake tallarsu cikin rana a titi da kasuwa

Jihar Sokoto - Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna na kasa, NAFDAC, ta kama mutane 24 da ke talla da sayar da magungunan kara karfin maza na gargajiya mara rajista a garin Sokoto.

Shugaban hukumar na jihar Sokoto, Garba Adamu, ya bayyana cewa NAFDAC ta kama motocci shida da na'urar amsa kuwwa da ake amfani da su wurin sayar da jabun magunguna.

NAFDAC ta kama mutane 24 da ke sayar da maganin ƙarfin maza a Sokoto
Maganin kara karfin maza da NAFDAC ta kama hannun mutum 24 a Sokoto. Hoto: Daily Nigerian
Asali: Facebook

Ya ce kayan da darajarsu ya kai Naira miliyan 2 an kwato su ne a kasuwanni da titunan birnin Sokoto.

Kara karanta wannan

An cafke wani sojan karya da abokinsa da ke samar wa da 'yan bindiga hanyoyin sadarwa

Ya ce za a tafi a yi wa magungunan da aka kwace gwaji sannan za a hukunta dukkan wadanda aka samu da hannu cikin lamarin don ya zama darasi ga wasu masu tallar.

Mista Adamu ya ce atisayen ya yi dai-dai ta umurnin da shugaban NAFDAC na kasa, Moji Adeyeye ta bayar na cewa tallar magungunan gargajiya a cikin rana ka iya janyo sauyawar sinadaren da ke cikinsu tare da kawo illa ga lafiyar mutane.

NAFDAC ta gargadi al'umma su guji shan magunguna marasa rajista

Ya yi kira ga al'umma su yi takatsantsan da magunguna marasa rajista, su kuma dena siyan kaya daga hannun masu tallar don taimkawa NAFDAC wurin tsare lafiyarsu.

A cewarsa, jami'an hukumar sun tsananta bincike a jihohin Kebbi da Sokoto ne domin tabbatar da ingancin kayayakin da ake sayarwa.

Kara karanta wannan

Yadda sojoji suka bankado yunkurin ISWAP na kai wa tubabbun Boko Haram farmaki

Ya kara da cewa za a cigaba da atisayen har sai an tsaftace harkar ya kuma yi kira ga masu magungunan gargajiya su rika bin dokokin gwamnati yayin gudanar da sana'arsu.

Mista Adamu ya jadadda cewa NAFDAC ba za ta yi kasa a gwiwa ba a kokarinta na tsare lafiyar 'yan Nigeria.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164