Yanzu-yanzu: Yan bindiga sun budewa motar dan majalisar wakilai wuta a Anambra, an kashe direbansa

Yanzu-yanzu: Yan bindiga sun budewa motar dan majalisar wakilai wuta a Anambra, an kashe direbansa

  • Yan bindiga sun sake kaiwa wani dan siyasa hari a yankin kudu maso gabas
  • Wasu yan bindiga da ake zargin matasan IPOB ne suka kai wannan hari
  • Wannan hari ya biyo bayan sauya shekar dan majalisan APC

Anambra - Wasu yan bindiga sun budewa tawagar motocin dan majalisar wakilan tarayya mai wakiltar mazabar Nnewi North, Nnewi South/Ekwusigo, Chris Emeka Azubogu, wuta a jihar Anambra.

Faifan bidiyon da ya bayyana a kafafen ra'ayi da sada zumunta ya nuna yadda abin ya faru a Nnobi a karamar hukumar Idemili South ta jihar.

Direbansa kadai ya mutu harin.

Hadimin dan majalisan, Ikechukwu Onyia, ya tabbatar da aukuwar lamarin inda ya bayyana cewa dan majalisan ba ya cikin motocin lokacin da aka kai harin.

TVCNews ta bayyana cewa yayinda ta tuntubi dan majalisan, ya tabbatar da mutuwar daya daga cikin direbobinsa a wannan mumunar hari.

Kara karanta wannan

VAT: Gwamnonin Arewa za su hada-kai da Gwamnatin Tarayya suyi shari’a da Jihohin Kudu

Dan majalisan na daya daga cikin yan majalisa a jihar Anambra 11 da suka koma jami'iyyar All Progressive Congress. (APC.) yau.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yan bindiga sun budewa motar dan majalisar wakilai wuta a Anambra, an kashe direbansa
Hoto: https:/www.tvcnews.tv
Yan bindiga sun budewa motar dan majalisar wakilai wuta a Anambra, an kashe direbansa Hoto: https:/www.tvcnews.tv
Asali: UGC

'Yan IPOB ne suka kashe mijin tsohuwar minista Dora Akunyili, tsohon jigon IPOB

Uche Mefor, mataimakin shugaban haramtacciyar kungiyar IPOB, ya zargi kungiyar da kisan Dakta Chike Akunyili a jihar Anambra.

Dakta Chike shine mijin marigayi Dora Akunyili, tsohuwar Ministar Yada Labarai da Sadarwa kuma Darakta-Janar na Hukumar Kula da Abinci da Magunguna ta Kasa (NAFDAC).

Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba sun harbe Dakta a ranar Talata 28 ga watan Satumba yayin da yake dawowa Enugu daga Onitsha, inda ya halarci lacca na tunawa da aka shirya don girmama marigayiyar matarsa.

Makasan mijin Dora Akunyili za su fuskanci hukuncin duniya da na Ubangiji, Buhari

Kara karanta wannan

Jihar Niger: Mayaƙan Boko Haram sun ratsa mazaɓu 8 cikin 25, Shugaban Ƙaramar Hukuma

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tabbatar wa da ‘yan uwan wadanda su ka rasa rayukan su a farmakin da ya yi sanadin mutuwar Dr Chike Akunyili cewa, duk masu alhakin kai farmakin za su fuskanci hukunci a nan da lahira.

Shugaban kasan ya bayar da wannan tabbacin ne ta wata takarda ta ranar Laraba wacce kakakin sa, Femi Adesina ya saki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng