El-Zakzaky: Mafi Yawancin Ƴan Nigeria Za Su Zaɓi Gwamnatin Shari'ar Musulunci Akan Gwamnatin Mu Mai Ci a Yanzu

El-Zakzaky: Mafi Yawancin Ƴan Nigeria Za Su Zaɓi Gwamnatin Shari'ar Musulunci Akan Gwamnatin Mu Mai Ci a Yanzu

  • Shugaban kungiyar musulunci ta Najeriya ta IMN, Sheikh Ibraheem El-Zakzaky ya ce ya tabbatar ‘yan Najeriya za su fi son shugabancin musulunci
  • A cewarsa, ya na da tabbacin idan za a bai wa ‘yan Najeriya da dama zabi za su zabi mulki bisa shari’ar musulunci akan wannan gwamnatin ta mu
  • Malamin ya zargi gwamnatin Najeriya da tauye ma sa hakkin sa na bil’adama ta hanyar hana sa zuwa kasar ketare don neman lafiya

Kano - Shugaban kungiyar musulunci ta IMN, Sheikh Ibraheem El-Zakzaky ya ce matsawar za a bai wa ‘yan Najeriya zabi, da dama za su gwammaci mulki bisa shari’ar musulunci akan wannan gwamnati ta mu.

Kamar yadda SaharaReporters ta ruwaito, shugaban ‘yan kungiyar Shi’a ya zargi gwamnatin tarayya da tauye ma sa hakkin sa ta hanyar hana shi ketarewa kasar waje don neman lafiya duk da fama da yake yi da ciwo a halin yanzu.

Kara karanta wannan

Yadda 'yan sandan Zamfara suka kama 'yan bindiga 69 da masu haɗa baki da su

El-Zakzaky: 'Yan Najeriya Da Dama Za Su Fi Son Gwamnatin Shari’ar Musulunci Bisa Wannan Gwamnatin
Sheihk Ibrahim El-Zakzaky, Shugaban Kungiyar IMN. Hoto: SaharaReporters
Asali: Facebook

Ya bayyana hakan ne yayin amsa tambayoyi lokacin da ake hira da shi a wani shirin gidan talabijin na Iranian Press TV a Kano ranar Laraba da yamma.

Wannan ne tattaunawar sa ta farko tun bayan an sako shi

Wannan shi ne tattaunawar sa na farko da gidan talabijin tun bayan an sake shi daga gidan gyaran hali a ranar 28 ga watan Yulin 2021 kamar yadda SaharaReporters ta ruwaito.

Dama an kama malamin kuma an rufe shi tun watan Disamban 2015.

Kamar yadda ya ce:

“Duk da an sake ni amma har yanzu a daure nake don sun ki ba ni damar fita kasar waje.”
Zakzaky ya bayyana yadda kungiyar sa take bukatar gwamnatin musulunci ta maye gurbin wannan gwamnatin, ta mulkin mallaka.

Kara karanta wannan

Lars Vilks: Mutumin da ya yi zanen ɓatancin Annabi Muhammadu a Sweden ya mutu a hatsarin mota

“Na yarda da cewa da za a sauya salon mulkin daga na turawan mulkin mallaka da aka gada zuwa na musulunci da ya fi.
“Na tabbatar idan aka bai wa ‘yan Najeriya zabi da yawa za su zabi tsarin musulunci.”

Sojoji Sun Yi Wa Mata 'Yan Shi'a Duka a Abuja, Sun Kama Wasu Da Dama

A wani labarin daban, sojoji sun yi wa wasu mata 'yan kungiyar Islamic Movement in Nigeria (IMN) da aka fi sani da shi'a duka a hanyar Abuja zuwa Kaduna a safiyar ranar Talata, Daily Trust ta ruwaito.

Sojojin da suka kafa shinge a wani wuri a babban titin sun tare wani mota da ke dauke da matan.

Nan take bayan fitowarsu daga motar, sojojin suka yi wa matan bulala tare da haurin su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164