Da Ɗumi-Ɗumi: Sojoji Sun Yi Wa Mata 'Yan Shi'a Duka a Abuja, Sun Kama Wasu Da Dama

Da Ɗumi-Ɗumi: Sojoji Sun Yi Wa Mata 'Yan Shi'a Duka a Abuja, Sun Kama Wasu Da Dama

  • Sojoji sun tare wasu motocci sun kama 'yan Shi'a a hanyar Abuja zuwa Kaduna
  • Wasu da abin ya faru a idonsu sun magantu kan yadda sojojin ke binciken motocci
  • Rahotanni sun ce sojojin sun yi wa wasu mata 'yan Shi'a bulala sannan suka tafi da su

Abuja - Sojoji sun yi wa wasu mata 'yan kungiyar Islamic Movement in Nigeria (IMN) da aka fi sani da shi'a duka a hanyar Abuja zuwa Kaduna a safiyar ranar Talata, Daily Trust ta ruwaito.

Sojojin da suka kafa shinge a wani wuri a babban titin sun tare wani mota da ke dauke da matan.

Nan take bayan fitowarsu daga motar, sojojin suka yi wa matan bulala tare da haurin su.

Da Dumi-Dumi: Sojoji Sun Yi Wa Mata 'Yan Shi'a Duka a Abuja, Sun Kama Wasu Da Dama
Da Dumi-Dumi: Sojoji Sun Yi Wa Mata 'Yan Shi'a Duka a Abuja, Sun Kama Wasu Da Dama
Asali: Original

Kara karanta wannan

Yadda jami'an tsaron UNIMAID suka afka dakunan kwanan dalibai mata, suka damke masu zanga-zanga

Daga bisani aka tafi da su cikin wani mota da aka yi parkin din ta a gefe.

Wakilin Daily Trust, wanda ke wurin da abin ya faru ya ce ya gano jami'an tsaro suna razana wasu fasinjojin da mutane da ke wucewa.

Sojojin suna bincika motocin da nufin neman mambobin kungiyar ta IMN.

"Ku fito yanzu! Kai ma daya daga cikinsu ne!" wani kakarfar soja mai girman jiki ya tsawatawa wani mutum da ke cikin motar bas.

Shaidan gani da ido ta tabbatar da afkuwar lamarin

Wata mata da ta nemi a sakayya sunanta, ta ce tana tare da wasu 'yan uwanta biyu a hanyarsu na zuwa tashar mota na Jabi a lokacin da aka tilastawa wasu fasinjoji da ke cikin motarsu fitowa.

Ta ce:

"Kafin mahaifiyata ta hau motar, an tilastawa direban da ya yi gaba. Ba mu samu damar taimaka mata ba sai dai kuka domin ba mu san halin da za ta shiga ba."

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Yan bindiga sun yi awon gaba da AVM Sikiru Smith (rtd) a jihar Legas

Daily Trust ba za ta iya tabbatar da adadin mutanen da aka kama ba a yanzu da ake hada rahoton.

Duk da haramta taro da tattaki da gwamnati ta yi wa 'yan Shi'a a Abuja, mambobin kungiyar suna cigaba da tattaki a titunan babban birnin kasar lokaci zuwa lokaci.

A ranar 28 ga watan Yulin 2021 ne babban kotun jihar Kaduna ta wanke Sheikh Ibraheem El-Zakzaky, shugaban IMN, daga zargin da ake masa bayan shafe shekaru 7 a tsare.

An kama shi ne bayan mabiyansa sun yi rikici da sojoji a Zaria, Jihar Kaduna a 2015.

Gwamnatin Jihar Kaduna ta tuhume shi da hannu a aikata kisa.

Kotu ta yanke hukuncin ɗauri ga matashin da ya kashe ƙanwarsa da duka saboda ta tara samari 6

A wani labarin daban, alkalin babbar kotun Bulawayo, da ke Zimbabwe, Justice Maxwell Takuva ya yanke wa wani saurayi mai shekaru 27 dan asalin Gweru a Zimbabwe shekaru 8 a gidan gyaran hali bayan ya yi wa kanwarsa mai shekaru 16 duka wanda ya yi sanadin mutuwar ta bisa zargin ta da rashin kamun kai.

Kara karanta wannan

Mutane 13 sun mutu a hatsarin mota a hanyarsu ta zuwa ɗaurin aure, ciki har da ƙanin ango da matarsa

Saurayin, Terrence Tarisai na Clifton Park ya musanta zargin da ake masa na halaka kanwar sa Tryphine, ya dake ta wanda har ta kai ga mutuwa bayan ya bincike sakonnin wayar ta na kafar sada zumuntar WhatsApp inda ya gano yarinyar ta tara samari har 6.

Asali: Legit.ng

Online view pixel