Da duminsa: FG ta ayyana Juma'a 1 ga watan Oktoba a matsayin ranar hutu

Da duminsa: FG ta ayyana Juma'a 1 ga watan Oktoba a matsayin ranar hutu

  • Gwamnatin tarayya ta sanar da Juma’a 1 ga watan Oktoba a matsayin ranar da hutun aiki don murnar cika shekaru 61 da samun ‘yancin kai
  • Ogbeni Rauf Aregbesola, ministan harkokin cikin gida ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba
  • Ministan ya yi amfani da wannan dama ya tabbatar wa ‘yan Najeriya kudurin gwamnati na magance dimbin kalubalen da kasar ke fuskanta

FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya ta ayyana ranar Juma’a, 1 ga watan Oktoba a matsayin ranar hutu don murnar shekaru 61 da samun ‘yancin kai.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa ministan cikin gida, Ogbeni Rauf Aregbesola ne ya bayyana hakan a madadin gwamnatin tarayya.

Da duminsa: FG ta sanar da ranar hutu don bikin 'yancin kai
FG ta ayyana Juma'a 1 ga watan Oktoba a matsayin ranar hutu Hoto: RAUF AREGBESOLA
Source: Facebook

Legit.ng ta tattaro cewa ministan ya taya al'umman Najeriya murnar shekaru 61 da samun ‘yancin kai sannan ya tabbatar da jajircewar gwamnati wajen magancewa tare da kawar da duk wasu kalubale da dukkan matsaloli da ke addabar kasar.

Read also

Yadda sojoji suka bankado yunkurin ISWAP na kai wa tubabbun Boko Haram farmaki

Kalaman Aregbesola na kunshe ne a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun sakataren din-din-din na ma'aikatar cikin gida, Dr Shuaib Belgore, a ranar Laraba, 29 ga watan Satumba, jaridar Vanguard ta ruwaito.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yace:

“Halinmu na kauna da iya tarban baki da kuma tarin dukiya ta al’umma da wadatar ƙasarmu, shakka babu shine yasa Najeriya ta zamo kan gaba a tsakanin bakaken fata a duniya sannan ta zamo abun alfahari da fatan Afrika, idan za mu iya haɗa kanmu tare don amfani da damarmu.
“Kasar da ke da mutum kusan miliyan 200 da doriya wadanda hazaƙarsu da begensu ke kyalkyali kamar lu’u lu’u mai daraja.
“Yan Najeriya suna walƙiya kamar lu'u -lu'u a kebabbe, imma a fannin Ilimi, Kasuwanci, tunani, Kiɗa, Fim, Nishaɗi, Yanayi da al'adu.
"Lallai mu ne kan gaba a baƙar fata a duk duniya kuma babu shakka alfahari da fatar Afirka."

Read also

DHQ ta karrama Laftanal Kanal Abu Ali, yariman da Boko Haram suka kashe a 2016

Bikin 'yancin kai: FG ta tsaurara matakan tsaro, za ta rufe sakatariya a ranar Alhamis 30 ga wata

A baya mun ji cewa, gabanin bikin cika shekaru 61 da samun ‘yancin kai, gwamnatin tarayya ta sanar da cewa za a rufe wasu sassan sakatariyarta da ke Abuja.

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa anyi hakan ne a wani bangare na kokarin tabbatar da bikin samun 'yancin kai a ranar Juma'a, 1 ga watan Oktoba cikin nasara.

Legit.ng ta tattaro cewa ginin sakatariyar yana kusa da dandalin Eagles Square kuma cewa za a gudanar da babban taro na 'yancin kai a ranar Juma'a a wajen.

Source: Legit.ng

Online view pixel