'Yan Bindiga Sun Kashe Mutum 20, Sun Sace Wasu Da Dama a Harin Da Suka Kai a Sokoto

'Yan Bindiga Sun Kashe Mutum 20, Sun Sace Wasu Da Dama a Harin Da Suka Kai a Sokoto

  • ‘Yan bindiga sun kai farmaki kauyen Gatawa dake karamar hukumar Sabon Birni a jihar Sokoto, kauyen da aka sani da zaman lafiya
  • Sun kai kazamin farmakin ne a ranar Talata da dare inda su ka halaka mutane 20 sannan su ka yi garkuwa da mutane da yawa
  • Lamarin ya auku ne bayan sa’o’i kadan da ‘yan bindiga su ka kai farmaki kauyen Gangara duk a karamar hukuma daya

Jihar Sokoto - A ranar Talata da dare ‘yan bindiga suka kai farmaki kauyen Gatawa dake karamar hukumar Sabon Birni a jihar Sokoto inda su ka halaka akalla mutane 20 sannan su ka sace wasu.

Kauyen yana daya daga cikin kauyaku mafi zaman lafiya a arewacin jihar inda ‘yan bindiga suke ta kai koma.

'Yan Bindiga Sun Kashe Mutum 20, Sun Sace Wasu Da Dama a Harin Da Suka Kai a Sokoto
Daya daga cikin matan da 'yan bindiga suka sace a yayin harin a Sokoto. Hoto: Premium Times
Source: Facebook

Read also

Tsohon Saurayi ya aikewa Ango tsaffin hotunan amaryarsa na lalata, aure ya mutu a daren farko

Sun kai farmakin ne bayan sa’o’i kadan da su ka kai farmaki kauyen Gangara wanda duk suke karkashin karamar hukuma daya.

Wani mazaunin yankin, Bashir Gobir, ya ce kanwar sa tana daya daga cikin wadanda aka yi garkuwa da su.

Wani ya ce wannan ne mafi munin farmaki a tarihi

Wata majiya wacce bata so a bayyana sunan ta ba tace wannan farmakin shine mafi muni.

Kamar yadda Premium Times ta ruwaito, majiyar ta ce:

“Sun iso ne a baburan su kamar yadda suka saba su na harbe-harbe. Sun shiga gida-gida su na neman abinci da sauran abubuwa sannan sun halaka mutane 20 sakamakon harin.”

Gobir ya ce bai san yawan mutanen da suka rasa rayukan su ba sakamakon harin.

A cewar sa:

“Yan bindigan sun kai farmaki Gatawa jiya da dare. Sun sace kusan komai mai daraja a kauyen sannan sun halaka mutane da dama sun kuma sace wasu. Kanwa ta, Rahila Galadima, tana daya daga cikin matan da suka sace."

Read also

Yadda jami'an tsaron UNIMAID suka afka dakunan kwanan dalibai mata, suka damke masu zanga-zanga

Yayin da aka nemi jin ta bakin kakakin ‘yan sandan jihar Sokoto, Sunusi Abubakar ya ce yana cikin wani taro kuma ya yi alkawarin kira daga baya kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Sai dai bai kira ba kuma be bayar da amsar sakon da aka tura ma sa ba.

Yayin tattaunawa da majiyar Legit.ng ta wayar salula, wani dan majalisar jihar mai wakiltar Sabon Birni ta kudu, ya ce yanzu farmakin ya addabi kowa.

Kamar yadda Premium Times ta ruwaito, ya ce:

“Abinda yake faruwa abin tashin hankali ne. Na san mutane da dama da aka halaka wasu kuma an ji musu raunuka sakamakon farmakin da aka kai Gangara.”

Source: Legit

Tags:
Online view pixel