Da dumi-duminsa: Hadimar Buhari ta bayyana sunayen makasan mijin tsohuwar minista

Da dumi-duminsa: Hadimar Buhari ta bayyana sunayen makasan mijin tsohuwar minista

  • An alakanta 'yan kungiyar masu fafutukar kafa kasar Biafra (IPOB) da kisan marigayi Chike Akunyili
  • Kai tsaye Lauretta Onochie ta zargi membobin haramtacciyar kungiyar na yankin kudu maso gabas da aikata kisan
  • Hadimar shugaban kasar kan harkokin yada labarai ta kuma bayyana cewa an kashe Akunyili tare da direba, fasto da kuma mai tsaron sa

A cewar Lauretta Onochie, mataimakiyar shugaban kasa kan harkokin yada labarai, mambobin kungiyar IPOB ne suka kashe marigayi Chike Akunyili, mijin Dora Akunyili a ranar Talata 28 ga watan Satumba.

Onochie ta yi wannan babban zargi a shafinta na Facebook a ranar Laraba, 29 ga watan Satumba.

Da dumi-duminsa: Hadimar Buhari ta bayyana sunayen makasan mijin tsohuwar minista
Hadimar Buhari ta bayyana sunayen makasan mijin tsohuwar minista Hoto: Vanguard
Source: Facebook

Hadimar shugaban kasar kan harkokin yada labarai ta kara da cewa an kashe mai tsaron marigayin, wani fasto da direbansa.

Read also

Tsohon Saurayi ya aikewa Ango tsaffin hotunan amaryarsa na lalata, aure ya mutu a daren farko

Ta ci gaba da bayyana cewa shi da sauran mutane sun je Onitsha don yin wani aiki na karrama marigayiyar matarsa Dora, ta kara da cewa kisan ya faru ne a lokacin dawowar su.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wallafarta:

“’Yan IPOB sun yiwa Dr Chike Akunyili, mijin marigayiya Dora Akunyili dinmu kisan gilla.
“An kuma kashe mai tsaronsa, wani fasto da direbansa.
"Ya je Onitsha ne don yin wani aiki na girmama marigayiya Dora. An kashe su ne a kan hanyarsu ta komawa gida.
"Da fatan Allah ya sa ya huta."
Da dumi-duminsa: Hadimar Buhari ta bayyana sunayen makasan mijin tsohuwar minista
Hadimar Buhari ta bayyana sunayen makasan mijin tsohuwar minista Hoto: Lauretta Onochie
Source: Facebook

Jerin abubuwa 3 masu ratsa zuciya da mijin tsohuwar minista yayi kafin a harbe shi

A halin da ake ciki, labari mai raɗaɗi na kisan Dakta Chike Akunyili, mijin marigayiya tsohuwar ministar watsa labarai, Farfesa Dora Akunyili, ya kasance tamkar fama miki ga 'yan Najeriya tsakanin Talata, 28 ga Satumba da Laraba, 29 ga Satumba.

Read also

Yadda jami'an tsaron UNIMAID suka afka dakunan kwanan dalibai mata, suka damke masu zanga-zanga

Wani amininsa da ya zanta da jaridar The Nation ya bayyana cewa marigayi Akunyili ya kasance tare da membobin kungiyar tsoffin daliban jami’ar Najeriya Nsukka (UNAA) a Sharon Hall, All Saints Cathedral, Onitsha, a ranar Talata sa’o’i kafin a kashe shi.

Majiyar ta lissafa kusan abubuwa uku da marigayin ya aikata kafin kisan nasa. Ya bayyana cewa yayin da yake ba da jawabinsa a taron, Akunyili ya yi magana cikin annashuwa game da ƙaunatacciyar matarsa ​​wacce mutuwa ta raba shi da ita a watan Yunin 2014.

Source: Legit

Online view pixel