An nada Sarkin Kano Uban Jami'ar Al-Istiqama dake Sumaila
- Sarkin Kano ya zaman uban jami'o'in Najeriya biyu yanzu
- Tsohon Dan majalisar wakilai ya nada shi Uban jami'arsa mai zaman kanta
- Farfesa Salisu Shehu ne Shugaban sabuwar jami'ar Sumaila
Kano - Hukumomin sabuwar jami'ar Al-Istiqama dake garin Sumaila, sun nada Mai Martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, a matsayin Uban jami'ar na farko tun bayan kafata.
Mu'assasin jami'ar, Alhaji Sulaiman Abdurrahmn Kawu Sumaila, tsohon dan majalisar wakilai ya sanar da hakan, rahoton DailyTrust.
Kawu Sumaila yace an nada Sarkin ne bisa gudunmuwar da yake badawa ga sashen Ilimi.
Yace:
"Hukumar jami'ar Al-Istikama Sumaila ta nada Mai Martaba Sarki Alhaji Aminu Ado Bayero matsayin Uban jami'ar na farko bisa dimbin gudunmuwar da yake baiwa bangaren Ilimi."
"Rawar da ya taka wajen assasa wannan jami'a na da muhimmanci."
Sarkin Kano a martaninsa, ya bayyana cewa zai yi iyakan kokarinsa wajen tabbatar da cigaba da nasarar jami'ar.
Yace:
"Ina godewa shugabannin jami'ar Al-Istiqama bisa wannan karramawa da suka yi min matsayin Uban jami'a na farko."
"Wannan karramawa ba nawa kadai bane, amma ga dukkan al'ummar jihar Kano da Masarautar."
Sarkin dai yanzu haka shine Uban jami'ar UNICAL bayan nadin da Buhari ya masa a watan Yuli.
Gwamnan jihar Kaduna ya nada Sarki Muhammadu Sanusi matsayin Uban jami'ar KASU
jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i, ya nada Sarkin Kano an 14, Muhammadu Sanusi na biyu, a matsayin sabon Cansalan Jami'ar jihar Kaduna KASU.
An nada tsohon Sarkin Kanon ne a taron yaye daliban jami'ar da akayi a ranar Asabar, 25 ga Satumba, 2021 a jihar Kaduna.
Gwamnan da kansa ya bayyana hakan a jawabin da ya saki a shafinsa na Facebook.
El-Rufa'i ya bayyana farin cikinsa na nada Sarki Sunusi wannan mukami.
Asali: Legit.ng