Gwamnan jihar Kaduna ya nada Sarki Muhammasu Sanusi matsayin Uban jami'ar KASU

Gwamnan jihar Kaduna ya nada Sarki Muhammasu Sanusi matsayin Uban jami'ar KASU

  • Tsohon Sarkin Kano ya sake samun mukami mai muhimmanci a Kaduna
  • Gwamnatin Kaduna ta yi bikin yaye daliban da suka kammala karatun digiri daban-daban a yau
  • Hakazalika an baiwa wasu manyan mutane kyautan digirin doktora na karramawa

Kaduna - Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i, ya nada Sarkin Kano an 14, Muhammadu Sanusi na biyu, a matsayin sabon Cansalan Jami'ar jihar Kaduna KASU.

An nada tsohon Sarkin Kanon ne a taron yaye daliban jami'ar da akayi a ranar Asabar, 25 ga Satumba, 2021 a jihar Kaduna.

Gwamnan da kansa ya bayyana hakan a jawabin da ya saki a shafinsa na Facebook.

El-Rufa'i ya bayyana farin cikinsa na nada Sarki Sunusi wannan mukami.

Gwamnan jihar Kaduna ya nada Sarki Muhammasu Sanusi matsayin Uban jami'ar KASU
Gwamnan jihar Kaduna ya nada Sarki Muhammasu Sanusi matsayin Uban jami'ar KASU Hoto: Nasir El-Rufa'i
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Cikin jahilci muka yiwa yan Najeriya alkawarin canji, yanzu mun fahimci Jonathan na da gaskiya: Jigon APC

Yace:

"An nada Mai Martaba Muhammadu Sanusi II matsayin Cansalan jami'ar jihar Kaduna (KASU), bayan haka kuma ya jagoranci taron yaye dalibai na hudu a jami'ar."
"Ina matukar farin cikin nada Sarkin Kano na 14, Muhammadu Sanusi II matsain Uban jami'ar Kaduna."
"Gwamnatin jihar Kaduna na farin ciki Muhammadu Sanusi II ya karbi wannan sabuwar nadi da mukayi masa."

Tattalin arzikin Najeriya ya na dab da durkushewa, Sanusi II

A bangare guda, tsohon gwamnan babban bankin Najeriya, Alhaji Muhammad Sanusi, ya ce tattalin arzikin Najeriya ya na dab da rushewa.

A yayin jawabi da yayi na ranar rufe gagarumin taron hannayen jari da aka yi a Kaduna mai taken KadInvest 6.0, Sanusi ya ce baya ga cewa Najeriya ta na da matsala wurin samar da mai, a yanzu kasuwannin duniya ba su siya.

Daily Trust ta wallafa cewa, tsohon sarkin Kanon ya ce "kyakyawar kazar da ke saka wa Najeriya kwai na dab da mutuwa."

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng