Aure yakin mata: Yadda uwar amarya ta duka kan gwiwowinta don rokon surukarta a kan ta kula mata da ‘yarta

Aure yakin mata: Yadda uwar amarya ta duka kan gwiwowinta don rokon surukarta a kan ta kula mata da ‘yarta

  • Wata mata ta taba zukatan mutane a kafafen sada zumunta bayan ta durƙusa don roƙon surukarta da ta kula da ɗiyarta
  • An gano uwar amaryar duke a gaban uwar ango a ranar daurin auren 'yarta kuma hakan ya taba zuciyar matashiyar
  • Yayin da mahaifiyarta ke rokon surukarta, amaryar ta kasa hana hawaye kwaranya daga idanunta kuma bidiyon ya haifar da martani mai yawa a shafukan sada zumunta

Wani bidiyo mai taba zuciya ya bayyana a kafafen sada zumunta inda aka gano uwar amarya ta durkusa don rokon surukarta da ta kula da 'yarta.

Matar 'yar Najeriya ta durƙusa a gaban uwar ango yayin da ake ɗaukar ɗiyarta zuwa dakin aurenta domin gina sabuwar rayuwa da masoyinta.

Yadda uwar amarya ta duka gwiwa bibbiyu don rokon surukarta a kan ta kula mata da ‘yarta
An gano uwar amarya duke bisa gwiwa bibbiyu don rokon surukarta a kan ta kula mata da ‘yarta Hoto: @instablog9ja
Source: UGC

A cikin bidiyon da @instablog9ja ya wallafa a shafin Instagram, ana iya ganin uban taron yana yi wa amarya addu’a, yana cewa babu wani sharri da zai same ta a sabon gidanta.

Read also

Tsohon Saurayi ya aikewa Ango tsaffin hotunan amaryarsa na lalata, aure ya mutu a daren farko

Mabiya shafin sun yi martani

Bidiyon ya taba zukata a kafafen sada zumunta kuma nan da nan mutane da yawa suka mamaye sashen sharhi na shafin don bayyana martanin su.

Mai amfani da Instagram tare da suna @olubori_o ya ce:

"Wataƙila ta fuskanci bakar wahala a hannun surukarta, kuma ba ta son irin haka ga 'yarta."

@sauceprince1 yayi sharhi:

"Akwai bukatar haka matuka. Domin abin da suke gani a shafukan sada zumunta a kwanakin nan ba wasa bane. Ni ma na durkusa, don Allah ku kula da matashiyar nan."

@lymaroyale ya rubuta:

"Ya kai a duka gwiwa har ƙasa. Wasu surukan daga ramin jahannama suke."

Mahaifi ya ƙwace ƴar shi bayan ta haifa ƴaƴa 5 saboda miji ya ƙi biyan sadaki

Read also

Yadda jami'an tsaron UNIMAID suka afka dakunan kwanan dalibai mata, suka damke masu zanga-zanga

A wani labari na daban, mahaifin matar wani Laban Sabiti, mai shekaru 29, mazaunin kauyen Bashayu a wuraren anguwar Rubanda a kasar Uganda, ya tasa keyar diyarsa mai yara 5 zuwa gida. Yanzu haka cikin yaran akwai jariri mai watanni 13 a duniya.

Sirikin sa, Geoffrey Kakona, mazaunin kauyen Karima a anguwar Kanungu, ya amshe diyarsa bayan Sabiti ya kasa biyan sadakin auren ta, LIB ta ruwaito.

Babban dan Sabiti ya kai shekaru 10 a duniya yayin da karamin har yanzu nono ya ke sha.

Source: Legit

Online view pixel