Nan da karshen shekara ‘Yan kwangila za su fara aiki a Mambilla, an gama komai inji Sanata
- Teslim Folarin ya yi bayanin abin da ya jawo bata lokaci a kwangilar Mambila
- ‘Dan majalisar yana sa rai nan da karshen shekara ‘yan kwangila su soma aiki
- Folarin ya bayyana cewa duk an shawo kan wasu matsaloli da ake fama da su
Abuja - A ranar Litinin, 27 ga watan Satumba, 2021, majalisar dattawan Najeriya tace shari’a a kotu suka hana a iya fara aikin wutar lantarkin Mambilla.
Jaridar Daily Trust ta rahoto ‘yan majalisar dattawan kasar suna cewa an magance duk wasu kalubale da suka jawo aka gaza fara yin wannan kwangila.
Majalisar dattawan tace ana sa ran ‘yan kwangila su isa yankin, su fara aiki kafin karshen shekara.
Teslim Folarin ya karbi rahoton kwamiti
Shugaban kwamitin da ya shafi irin wadannan ayyukan a majalisar, Sanata Teslim Folarin, ya yi wannan bayani da yake karbar wani rahoton aikin kwangilar.
Teslim Folarin yace an gamu da cikas ne saboda sai da hukumar da ke kula da cigaban yankin Arewa maso gabashin Najeriya ya sake duba wannan aikin.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
‘Dan majalisar yace NEDC ta kawo takardun aikin da TWG suka yi a kan yadda za a yi kwangilar.
Kamar yadda jaridar ta Daily Trust ta rahoto, Folarin yace an gabatar da wadannan takardun a gaban majalisar tarayya domin a dauki matakin da ya dace.
"Bayan nan majalisar tarayyan da kwamitin TWS sun kafa wani karamin kwamiti da zai kula da harkar kudi a karkashin jagorancin shugaban bankin NEXIM."
"A shekarar nan aka kaddamar da kwamitin, kuma aka ce ya gabatar da rahoto a makonni shida."
"Wannan kwamiti ne aka ba nauyin tsara yadda za a samu kudin yin kwangilar, ana lissafin Naira biiliyan 1.7, wanda shi ne 30% na kudin kwangilar, $5.7bn."
“Ba ni da wani haufi cewa duk an shawo kan wadannan da ma wasu abubuwan, kuma nayi imani za a samu takarda a kan yadda za a iya aiwatar da aikin.”
An kai karar gwamnatin Najeriya
A watannin baya ku ka ji cewa aikin Mambilla ya dawo baya saboda kamfanin Sunrise Power Transmission Company of Nigeria ya tafi kotu, yana karar gwamnati.
Sunrise Power Transmission Company of Nigeria yana so a biya shi dala biliyan 400. Kamfanin na neman wadannan kudi ne saboda saba wa yarjejeniyar da aka yi.
Asali: Legit.ng