Abin Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Sabuwar Fasahar 5G, Masani Daga Kano Ya Yi Fashin Baƙi

Abin Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Sabuwar Fasahar 5G, Masani Daga Kano Ya Yi Fashin Baƙi

  • Kamfanin Huawei na ƙasar China ne ta fara ɓullo da fasahar sadarwar ta 5G
  • Babu wani sahihin binciken da ya tabbatar 5G na yaɗa korona ko janyo cutar daji
  • Fasahar 5G za ta kawo sauye-sauye masu amfani a ɓangarorin rayuwa da dama

Mallam Shehu Auwal masanin fasahar sadarwar zamani da kwamfuta, mazaunin Kano a Nigeria.

A cikin ƴan kwanakin nan ne ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Isa Ali Pantami sanar da cewa za a fara aiki da fasahar 5G a kasar a watan Janairun 2022.

A kan wannan gabar ne Legit.ng Hausa ta tuntunbi masanin fasahar sadarwa zamani da kwamfuta, Mallam Shehu Auwal mazaunin Kano don yin fashin baƙi game da batun.

Kara karanta wannan

Tsohon Saurayi ya aikewa Ango tsaffin hotunan amaryarsa kan ta tuba, aure ya mutu

Abin Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Sabuwar Fasahar 5G, Masani Daga Kano Ya Yi Fashin Baƙi
Abin Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Sabuwar Fasahar 5G, Masani Daga Kano Ya Yi Fashin Baƙi. Hoto: Daily Trust
Asali: Twitter

Da farko dai wakilin Legit.ng Hausa ya fara masa tambaye ne kan menene ake nufi da fasahar 5G?

Shehu Auwal ya bada amsa kamar haka:

"Toh shi 5G fasaha ce tamkar cigaba kan harkar sadarwa wato network, a baya ana amfani da wasu wayoyi ne da ake kira 'dial of connection' da ake latsa su kafin a samun damar hawa intanet.
"Daga baya kuma aka fara samun cigaban network irin gprs, sai aka samu edge, sannan aka samu 3G kana 4G ta fito."

A cewar Auwal, ko wacce fasaha ta fi wadda ta gabace ta sauri, ma'ana ana samun cigaba kenan da ɓunkasa fasahar sadarwar.

Ta yaya aka samu ɓullar 5G?

Kamfanin Huawei da ZTE na ƙasar China ne suka fara fitowa da sabuwar fasahar ta 5G.

Kara karanta wannan

Yadda jami'an tsaron UNIMAID suka afka dakunan kwanan dalibai mata, suka damke masu zanga-zanga

Amma a baya, kamfanonin sadarwa na kasar Amurka ne ke ƙirƙirar fasahar 2G, 3G da sauransu.

Hakan kuma na nufin kamfanin na Huawei za ta samu riba sosai idan mutane suka fara amfani da fasahar.

Wane irin amfani fasahar 5G zai yi wa al'umma?

Kamar yadda Mallam Auwal ya bayyana, fasahar 5G ya ɗara 4G wurin sauri sosai ta yadda likita daga ƙasar waje zai iya yin tiyata ba tare da ya iso Nigeria ba.

Hakan zai yiwu ne saboda za a sada shi ta intanet yana kallon duk abin da ke faruwa kuma ba za a samu tsaiko ba.

Hakazalika, a ɓangaren wurin sauke bidiyo ko kallonsa a intanet wato streaming, idan 5G ne za a samu matukar sauri ta yadda misali mutum na iya sauke bidiyon 2GB ko 3GB cikin awanni ko mintuna 30 zuwa 40, idan a 5G ne ba zai wuce minti 10 ko 5.

Ta yaya 5G zai shafi tattalin arzikin Nigeria? Kuɗin data na iya sauya wa?

Kara karanta wannan

Rikicin Zamfara: Akwai hannun tsofaffin Gwamnoni, ya kamata a tsige Sarakuna 15

"Fasahar 5G baya nufin farashin data zai canja, cikin data da mai amfani ke siya dai za a cire dai-dai abin da ya yi amfani a bar masa sauran" a cewar Auwal.

Menene alakar 5G da cutar korona ko wasu cututtukan?

Da aka masa tambaya kan cewa fasahar ta 5G tana janyo wata cuta ko asassa wasu cututtukan, masanin ya kada ba ki ya ce:

A fahimta ta duk zargin da ake yi na alakanta 5G da wasu cututtuka labarai na marasa hujja ko tushe, ma'ana dai kawo yanzu babu wani sahihin bincike da ya nuna 5G na janyo cuta.

Auwal ya ce ko a ƙasar Birtaniya da za a yi gwajin fara amfani da 5G, gwamnatin Birtaniya ta yi amfani da ƴan kasarta ne saboda rashin amincewa da China bisa zargin za ta iya amfani da fasahar don leƙen asiri.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Tags: