Gwamnonin Arewa sun yi kuskure, kundin tsarin mulki ya halatta tsarin kama-kama, Lauya

Gwamnonin Arewa sun yi kuskure, kundin tsarin mulki ya halatta tsarin kama-kama, Lauya

  • Lauya ya bayyana cewa gwamnonin Arewa sun jahilci kundin tsarin mulkin Najeriya
  • Lauyan yayi martani ne kan shawarar da gwamnonin suka yanke jiya a Kaduna
  • Da alamun an ja layin daga tsakanin gwamnonin Arewa da na kudancin Najeriya

Shahrarren Lauya, Ebun-Olu Adegboruwa (SAN), ya bayyana cewa kundin tsarin mulkin Najeriya ta 1999 ta halalta tsarin kama-kama na mukamin shugabancin kasa.

Hakazalika ya ce kundin tsarin mulkin ta haramta yanki daya tayi kane-kane kan mulki ta hana saura danawa.

Hakazalika Adegboruwa yace akwai rashin adalci cikin maganar gwamnonin Arewa da sukayi bayan taronsu a jihar Kaduna ranar Litinin cewa kundin tsarin mulki bai san tsarin kama-kama.

Babban lauyan ya bayyana hakan ne ranar Talata yayinda ya bayyana a shirin 'Sunrise Daily' na tashar ChannelsTV.

Yace:

"La'alla gwamnonin basu samu shawara mai kyau wajen lauyoyinsu bane kan kundin tsarin mulkin Najeriya da ma kundin tsarin jam'iyyunsu kafin kalamai irin wannan na cewa tsarin kama-kama bai hallata ba."

Read also

Tsohon Saurayi ya aikewa Ango tsaffin hotunan amaryarsa na lalata, aure ya mutu a daren farko

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Sashe 14 na kundin tsarin mulkin 1999, musamman 14(3), yayi magana kan raba mukaman gwamnati ta yadda jiha daya ko kabila guda ba zata fi saura ba
"Saboda haka idan gwamnoni suka bayyana cewa tsarin kama-kama ya sabawa kundin tsarin mulki, sashen da sukayi la'akari da shi yana magana ne kan tsarin zabe, yadda ake zaben shugaban kasa."

Gwamnonin Arewa sun yi kuskure, kundin tsarin mulki ya halatta tsarin kama-kama, Lauya
Gwamnonin Arewa sun yi kuskure, kundin tsarin mulki ya halatta tsarin kama-kama, Lauya Hoto: Simon Lalong
Source: Facebook

Gwamnonin Arewa sun maida wa na Kudu raddi kan batun fito da Shugaban Najeriya a 2023

Gwamnonin Arewacin Najeriya sun maida martani game da ikirarin takwarorinsu na kudu a kan cewa dole sai shugaban kasa ya fito daga yankinsu.

Gwamnonin jihohin Arewacin kasar sun yi raddi a zaman da suka yi ranar Litinin, 27 ga watan Satumba, 2021 a jihar Kaduna.

Kungiyar gwamnonin Arewa ta fitar da matsaya, tace babu inda doka tace dole mulki ya koma kudu.

Read also

Yadda jami'an tsaron UNIMAID suka afka dakunan kwanan dalibai mata, suka damke masu zanga-zanga

A karshen taron gaggawan da aka yi a gidan gwamnatin Sir Kashim Ibrahim House a Kaduna, kungiyar tayi tir da kalaman da gwamnonin kudu suka yi a baya.

Shugaban kungiyar gwamnonin yankin, Simon Bako Lalong yace abin da gwamnonin jihohin kudancin Najeriya suke fada ya ci karo da kundin tsarin mulki.

Source: Legit.ng

Online view pixel