Gwamnonin Arewa sun maida wa na Kudu raddi kan batun fito da Shugaban Najeriya a 2023

Gwamnonin Arewa sun maida wa na Kudu raddi kan batun fito da Shugaban Najeriya a 2023

  • Gwamnonin Arewa sun yi zaman gaggawa a ranar Litinin a garin Kaduna
  • A taron da aka yi, gwamnonin sun maida wa takwarorinsu na Kudu raddi
  • Gwamnonin Kudu sun fito suna cewa dole su za su fito da Shugaban kasa

Kaduna – Gwamnonin Arewacin Najeriya sun maida martani game da ikirarin takwarorinsu na kudu a kan cewa dole sai shugaban kasa ya fito daga yankinsu.

Daily Trust ta fitar da rahoto cewa gwamnonin jihohin Arewacin kasar sun yi raddi a zaman da suka yi ranar Litinin, 27 ga watan Satumba, 2021 a jihar Kaduna.

Kungiyar gwamnonin Arewa ta fitar da matsaya, tace babu inda doka tace dole mulki ya koma kudu.

A karshen taron gaggawan da aka yi a gidan gwamnatin Sir Kashim Ibrahim House a Kaduna, kungiyar tayi tir da kalaman da gwamnonin kudu suka yi a baya.

Kara karanta wannan

Yadda jami'an tsaron UNIMAID suka afka dakunan kwanan dalibai mata, suka damke masu zanga-zanga

Ko da wasu gwamnonin sun nuna goyon-bayansu ga komawar mulki kudu a 2023, kungiyar tace ana daukar wannan matsayar ne domin a samu zaman lafiya.

Gwamnonin Arewa
Gwamnonin Arewa a Kaduna Hoto: NGF
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Shugaban kungiyar gwamnonin yankin, Simon Bako Lalong yace abin da gwamnonin jihohin kudancin Najeriya suke fada ya ci karo da kundin tsarin mulki.

“Jawabin ya ci karo da tsarin mulkin Najeriya na shekarar 1999 da aka yi wa garambawul.”
“Doka tace shugaban kasar da za a zaba sai ya samu akalla 25% na kuri’un da aka kada wa a kashi biyu bisa ukun jihohin tarayya.”

Gwamnan na Filato wanda shi ne shugaban kungiyar, yace idan zabe ya kai ga zagaye na biyu, abin da ake bukata shi ne wanda ya fi samun kuri’a, ya ci zabe.

Kamar yadda jaridar ta kawo rahoto dazu da rana, a jawabinsa, gwamnan Filato, Simon Bako Lalong, yace ba za su amince da abin da takwarorinsu suke yi ba.

Kara karanta wannan

Tattalin Arzikin Arewa Maso Gabas Yana Daf Da Durƙushewa, NPYA Ta Yi Gargaɗi

Siyasar cikin gidan PDP

A ranar Litinin muka kawo maku rahoto game da dalilin PDP na kai kujerar shugaban Jam’iyya Kudu, sannan aka yarda a ba 'Yan Arewa tutar shugaban kasa

Gwamnan Ribas, Nyesom Wike ne kurum ake zargin yana da ra’ayin da ya sha ban-bam. Bisa dukkan alamu hakan bai rasa nasaba da burinsa na yin takara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng