Na rasa manyan abokai saboda goyon bayan Zulum kuma bana nadaman hakan, Kashim Shettima

Na rasa manyan abokai saboda goyon bayan Zulum kuma bana nadaman hakan, Kashim Shettima

  • Sanata Shettima ya bayyana yadda wasu abokansa suka juya masa baya kan Zulum
  • Shettima yace ko gobe ya samu dama sai ya sake zaben Zulum
  • A cewarsa, Zulum mutum ne mai gaskiya kuma ma kokari

Tsohon Gwamnan jihar Borno kuma Sanata mai wakiltan Borno ta tsakiya, Kashim Shettima, yayi waiwaye kan lokacin da alanta Zulum a matsayin wanda zai goyi baya a zaben fiddan gwamnan jam'iyyar APC a 2019.

Kashim ya bayyana cewa wannan shawara da ya yanke ta sanya shi asarar manyan abokan da ya dade yana hulda da su.

Shettima yayi tsokaci ne kan jawabin da yayi na goyon bayan Zulum.

A cewar Shettima, ashe dukkan masu yi masa biyayya na ikirarin soyayya duk makaryata ne, kawai kansu suke yi mawa.

Shettima yace:

Read also

NSCDC ta kama mutumin da ke taimakawa masu garkuwa karɓar kuɗin fansa

"Facebook ta tuna min jawabin da nayi shekaru uku da suka gabata. Tabbas na yi rashin abokai da muka kwashe gomman shekaru tare saboda wannan shawara."
"Da yiwuwan ma wadanda mutanen da nikewa kallon abokai ba dan Allah ake zaman tare ba. Ashe kansu kawai suke yi mawa. Biyayya, soyayya da sukeyi ashe duk karya ne."

Na rasa manyan abokai saboda goyon bayan Zulum kuma bana nadaman hakan, Kashim Shettima
Na rasa manyan abokai saboda goyon bayan Zulum kuma bana nadaman hakan, Kashim Shettima Hoto: Governor of Borno
Source: Facebook

Ban na nadamar zaben Zulum, ko gobe idan ina da dama zan sake zabensa, Shettima

Gwamna Shettima ya kara da cewa sam bai yi nadamar zaben Gwamna Babagana Zulum ba saboda ko gobe ya sake samun dama zai yi hakan.

Shettima yace Zulum mutum ne mai gaskiya kuma duk wanda bai yarda da hakan ba ya je ya kashe kansa.

A cewarsa:

"Wannan lamarin Borno ne kuma idan na samu dama, ba zan canza shawara ba."

Read also

Gwamnan Arewa ya yi iƙirarin wasu manya sun daƙo hayar masu kisa daga ƙasar waje su kashe shi

"Gwamna Zulum mutum ne mai gaskiya kuma abokin kwarai. Duk wanda ke ganin sabanin haka yaje ya ga fada cikin tekun Atlantic."

An siyasantar da diban ma'aikatan tsaro, Gwamna Zulum ya koka

Gwamna Babagana Umara Zulum ba jihar Borno a ranar Laraba ya zargi daukan jami'an tsaro da hukumomin tsaron Najeriya ke yi aiki da saka siyasa a lamarin, abinda ke saka fannin tsaron kasar nan cikin mawuyacin hali.

Zulum na yin jawabi ne a NIPSS da ke Kuru, jihar Filato, Daily Trust ta wallafa.

Source: Legit.ng

Online view pixel