Kotu ta yanke hukuncin ɗauri ga matashin da ya kashe ƙanwarsa da duka saboda ta tara samari 6

Kotu ta yanke hukuncin ɗauri ga matashin da ya kashe ƙanwarsa da duka saboda ta tara samari 6

  • Kotu a Zimbabwe ta yanke wa saurayi mai shekaru 27 daurin shekaru 8 a gidan gyaran hali
  • Hakan ya biyo bayan dukan kawo-wuka da ya yi wa kanwar sa mai shekaru 16 daga nan ta rasu
  • Matashin ya zarge ta da soyayya da samari 6 duk da kasancewar ta karamar yarinya

Zimbabwe - Alkalin babbar kotun Bulawayo, da ke Zimbabwe, Justice Maxwell Takuva ya yanke wa wani saurayi mai shekaru 27 dan asalin Gweru a Zimbabwe shekaru 8 a gidan gyaran hali bayan ya yi wa kanwarsa mai shekaru 16 duka wanda ya yi sanadin mutuwar ta bisa zargin ta da rashin kamun kai.

Kotu ta yanke hukuncin ɗauri ga matashin da ya kashe ƙanwarsa da duka saboda ta tara samari 6
Alkali ya yanke wa matashin da ya halaka kanwarsa saboda tana da samari 6 hukuncin daurin shekaru 8. Hoto: LIB
Asali: Facebook

Saurayin, Terrence Tarisai na Clifton Park ya musanta zargin da ake masa na halaka kanwar sa Tryphine, ya dake ta wanda har ta kai ga mutuwa bayan ya bincike sakonnin wayar ta na kafar sada zumuntar WhatsApp inda ya gano yarinyar ta tara samari har 6.

Kara karanta wannan

Tsoho mai shekaru 84 da ya bar gida tsawon shekaru 47 ya dawo, ya nuna ɓacin ransa don matansa 2 sun sake aure

Ya dake ta ne bayan ya dawo gida bai tarar da ita ba

Kamar yadda LIB ta ruwaito, an samu rahotanni akan yadda Tarisai ya dawo gida ranar 22 ga watan Yulin 2020 bai ga Tryphine ba inda ta bar kanwar ta mai shekaru 10 ita kadai a gida.

Tryphine wacce ‘yar aji 3 ce a Ascot High School dake Gweru ta dawo gida karfe 6 na yamma. Ta bayyana wa yayan ta cewa a shago ta tsaya.

Saidai Tarisai bai yarda da bayanin ta ba ya kwace wayar ta ya bincike sakonnin ta na WhatsApp inda ya gane ta na tara samari da yawa. Daga nan ya zarge ta da rashin kamun kai.

Ganin hakan ne ya sa Tryphine ta gudu gidan antin ta dake Mtapa yanki na 7 a Gweru. Washegari da safe antin Tryphine ta raka ta gida.

Kara karanta wannan

Daga 1 ga watan Oktoba matsalolin Najeriya za su kau, inji hasashen wani Fasto

Sai da ya yi mata duka kashi biyu

Duk da antin ta yi masa magana kuma ta bashi hakuri sai da ya samu wata bulala ya yi mata dukan tsiya kuma ya bukaci ta dakatar da alakar ta da duk samarin ta. Daga nan ya ci gaba da dukan ta.

Bayan ta sha duka kamar bakuwar karya, sai Tryphine ta fara korafin tana jin sanyi don hakan antin ta ta daura ta a gado don ta huta. Daga nan ne ta rasu bayan ta kwashe sa’o’i tana bacci. Bayan an gano ta rasu ne ‘yan sanda su ka kama Tarisai.

Alkalin kotun da ya yi hukunci ya ja kunnen jama’a akan amfani da karfi wurin tankwasa yara. Kamar yadda LIB ta ruwaito, Justice Takuva ya ce:

“Akwai bukatar iyaye da magabata su dena amfani da karfi mai yawa wurin tankwasa yara saboda hakan ya ja an rasa rayuka da dama. Ga shi yanzu an rasa ran yarinya karama. Sakamakon dukan cutarwa da ya yi mata an yanke ma sa hukuncin shekaru 8 a gidan gyaran hali."

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Bincike ya nuna abinda ya kashe budurwar da aka tsinci gawarta cikin motar basarake da ya tsere

Kano: Hotunan ɓarayin waya uku da aka kama bayan sun kashe wani sun ƙwace wayansa

A wani labarin daban, rundunar ‘yan sanda ta jihar Kano ta kama wasu mutane 3 da ake zargin sun sharba wa wani Mohammed Sulaiman wuka inda hakan ya kai ga ajalin sa sannan suka gudu da wayar sa.

Kamar yadda LIB ta ruwaito, sun kara da bayyana cewa sun kai wa wani Kingsley farmaki a ranar Lahadi inda suka kwace wayar sa kuma suka tsere.

Kakakin rundunar, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa a wata takarda ta ranar Litinin, 20 ga watan Satumba ya ce sun kama wadanda ake zargin bisa laifin fashi da makami.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164