Gwamna ya sanya N20m ga duk wanda ke da bayanai kan kashe mijin Dora Akunyili
- Gwamnan jihar Anambra ya ba da sanarwar cewa zai ba da ladar N2Om ga duk wanda ya ke da bayanai kan kisan Dakta Akunyili
- Ya kuma nemi hadin kan matasa da sarakunan gargajiya a yankin da su taimaka wajen kare mutanen yankinsu
- Karshe ya tura sakon ta'aziyya ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu, kana ya yi mamatan addu'ar salama
Anambra - Gwamna Willie Obiano ya sanar da ba da ladar Naira miliyan 20 ga duk wanda ke da bayanai masu amfani da za su kai ga cafke wadanda ke da hannu a kisan gillar Dakta Chike Akunyili da sauran munanan hare-hare a jihar Anambra.
A yau ne aka tashi da labari mara dadi da ke cewa, wasu 'yan bindiga sun harbe Dakta Chike Akunyili, mijin wata jigo a gwamnatin baya, Dora Akunyili.
Gwamnan na Anambra ya bayyana haka ne lokacin da yake jawabi a shafinsa na Facebook a ranar Laraba, 29 ga watan Satumba.
Obiano ya koka kan yadda wasu 'yan ta'adda dauke da makamai suka kaddamar da ta’addanci tare da kai hare-hare kan ‘yan kasa a sassa daban-daban na jihar a cikin 'yan kwanakin da suka gabata.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
An kashe mutane 10 cikin kwanaki uku
Gwamna Obiano ya lura cewa an kashe mutane 10 a sassa daban-daban na jihar tsakanin ranar Lahadi, 26 ga Satumba zuwa Talata, 28 ga Satumba, ciki har da Dr Chike Akunyili, mijin marigayiya Farfesa Dora Akunyili.
Ya kara da cewa an kai hari ofisoshin wasu jam’iyyun siyasa a jihar, gami da motocin yakin neman zabe da kuma mutanen da ke cikinsu, tare da kashe-kashe da kona motocin.
Obiano ya nemi hadin kan matasa da sarakunan gargajiya
Gwamnan na Anambra ya kuma yi kira ga dukkan matasan jihar da su tashi su kare al'ummomin su.
Ya kuma nemi sarakunan gargajiya, malaman addini, kungiyoyin 'yan banga da dukkan masu jagoranci a jihar da su dauki nauyin taimakawa hukumomin tsaro don dawo da doka da oda cikin gaggawa.
Ta'aziyya ga iyalan wadanda suka yi rashi
Gwamna Obiano ya kuma jajantawa iyalan dukkan wadanda suka rasa 'yan uwansu sanadiyyar munanan hare-haren.
Ya yi alkawarin cewa gwamnatinsa ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen samar da adalci a gare su tare da yi musu addu'ar Allah ya ba su zaman lafiya.
Asali: Legit.ng