Sule Lamido Ya Magantu Kan Rashin Tsaro: Ba Bu Shugabanci a Nigeria
- Tsohon gwamnan jihar Jigawa Sule Lamido ya yi magana kan batun rashin tsaro a Nigeria
- Lamido ya ce matsalar da ake fama da ita shine babu jagoranci na gari a kasar don wadanda ke mulki ba su san yadda za su yi ba
- Tsohon gwamnan na Jigawa ya ce jam'iyyar APC ta yi wa matasa karya lokacin zabe yanzu kuma ta gaza cika alkawurran
Sule Lamido, tsohon gwamnan jihar Jigawa ya ce Nigeria ba ta da shugabancin da ake bukata domin tunkarar kallubalen rashin tsaro a kasar, The Cable ta ruwaito.
A yayin da ake zantawa da shi a shirin 'Sunday Politics' a gidan talabijin na Channels, a ranar Lahadi, Lamido ya ce ya zama dole gwamnati ta rika fadawa mutane gaskiya.
Ya ce:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Ya kamata mutane su rika bibiyar gwamnati kan alkawurran da ta yi kuma bana son ya zama kaman na saka siyasa cikin lamarin amma gaskiya ne. Idan kana neman mulki na siyasa ya kamata hanyar samun ya zama nagartace."
"Ya kamata mu ajiye siyasa a gefe. Mene mu ke yi a matsayin mu na shugabanni? Ba mu da shugbanci a Nigeria, wannan shine matsalar kuma duniya na kallon mu.
"Fiye da komai, matsalar shine shugabanci. Shugabanci na gari na da matukar muhimmanci. Me yasa Zamfara ke zama matattaran ta'addanci a Nigeria, Me yasa?"
Jam'iyyar APC ta nemi mulki ne ba tare da sanin abin da za ta aiwatar ba
A cewar rahoton na The Cable, Lamido ya ce jam'iyyar APC mai mulki ba ta da wani tsarin kawo canji kawai mulki ta ke so a 2015.
Ya ce:
"Sun san karya suke yi. Kafin nan, mulki kawai ake so. Sai bayan sun samu mulki sannan suka fara tambaya, me za mu yi? Don haka tun farko ya kamata a saka adalci a lamarin."
"Batun shine halin yi wa matasa karya.
"Idan ka saka musu rai cewa gwamnati za ta taimaka musu, ka samu gwamnati kuma ka gaza biya musu bukatunsu, za a samu matsaloli."
Sule Lamido: Najeriya ba zata taɓa cigaba ba, har sai PDP, APC sun daina tunanin mulki
A wani labarin daban, tsohon gwamnan Jigawa, Sule Lamido, ya zargi manyan jam'iyyun ƙasar nan APC da PDP da jefa Najeriya cikin halim ƙaƙanikayi, kamar yadda Premium times ta ruwaito.
A wata fira da Channels TV ranar Lahadi, tsohon gwamnan yace matsalolin Najeriya na ƙaruwa ne saboda mugun kwaɗayin mulkin shugabannin APC da PDP, mai makon saka cigaban ƙasa a gaba.
Bugu da kari, jigon PDP, Lamido, ya bayyana cewa dama tun farko ya yi hasashen haka zata faru ƙarƙashin mulkin jam'iyyar APC.
Asali: Legit.ng