Taliban: Gwamnatin mu za ta dawo da datse hannun ɓarayi da sauran hukunce-hukuncen shari'ar musulunci
- Tsohon shugaban ‘yan sandan addini na Taliban ya ce za su ci gaba da yanke hukunce-hukuncen da suka saba a Afghanistan
- Mullah Nooruddin Turabi wanda yanzu shi ne yake kula da gidajen yari ya ce wajibi ne su dinga datse wa masu laifi gabobi
- A cewar sa ba lallai su dinga yi gaban mutane ba kamar yadda su ka yi a baya amma zasu yi hukuci kuma babu mai dakatar da su
Afghanistan - Tsohon shugaban ‘yan sandan Taliban yace za su ci gaba da hukunce-hukunce kamar yanke gabobin masu laifi a Afghanistan.
Kamar yadda Arise Tv ta ruwaito, Mullah Nooruddin Tarabi wanda shine mai kula da gidajen yarin kasar Afghanistan ya sanar da AP News cewa wajibi ne su ci gaba da hukunce-hukuncen saboda tsaro.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ya ce babu mai dakatar da su
A cewar sa ba lallai a dinga hukuncin a gaban mutane ba kamar yadda suke yi a baya.
A cewar sa:
“Babu wanda ya isa ya fada mana abinda ya dace mu yi.”
Tun bayan Taliban sun amshi mulkin Afghanistan a ranar 15 ga watan Augusta su ka yi alkawarin ci gaba da hukuncin da suka saba a baya amma da dan sassauci.
Saidai an samu rahotanni akan yadda suke keta hakkin bil’adama a fadin kasar.
A ranar Alhamis, masu rajin kare hakkin bil’adama sun bayyana yadda Taliban a Herat suke hana mata su na hana su fita daga gidajen su sannan su tursasa su sanya sutturun da dokar su ta tanadar.
Ana saura ‘yan kwanaki Taliban su amshi Kabul, babban alkalin Taliban a Balkh, Haji Badruddin ya sanar da BBC cewa yana bai wa Taliban goyon baya dari bisa dari wurin zartar da hukuncin shari’ar musulunci.
Za su ci gaba da datse wa barayi hannu su na zane mazinata
Kamar yadda Arise TV ta ruwaito ya ce:
“Kamar yadda shari’ar mu ta tanadar, duk saurayi ko budurwa suka yi zina, za a yi musu bulalai 100 a gaban kowa.”
“Amma ga masu aure kuwa, za a jefe mutum har sai ya mutu. Duk wanda aka kama ya yi sata kuma aka tabbatar, za a datse masa hannun sa.”
Kamar yadda Turabi, wanda tsohon ministan shari’a ne ya bayyana a wata tattaunawa da aka yi da shi:
“Kowa yana ta caccakar mu akan yanke hukunci a bainar jama’a, sai dai bamu taba cewa komai ba dokoki da kuma hukuncin kowa.”
A farkon wannan makon, Taliban sun bukaci su yi jawabi a wani taro da aka yi a majalisar dinkin duniya, wanda aka yi a birnin New York.
Ministan harkokin kasashen ketare na Jamus ya ce yana da kyau a tattauna da mayakan Taliban sai dai ba a majalisar ne yafi dacewa ayi hakan ba.
Sarkin Katsina ya barranta da matsayar Sheikh Gumi: Kisa ya dace da ƴan bindiga ba tattaunawa da su ba
A wani labarin daba, mai martaba Sarkin Katsina ya ce tunda ƴan bindiga sun zaɓi su rika kashe mutane 'suma bai dace a bar su da rai ba'.
Sarkin na Katsina, Abdulmuminu Usman ya ce ba abin da ya dace da ƴan bindigan da ke kashe mutane a arewa maso yamma illa kisa.
Sarkin ya yi wannan furucin ne yayin taron tsaro na masu ruwa da tsaki a ranar Talata a Katsina kamar yadda Premium Times ta ruwaito.
Asali: Legit.ng