Katsina: Jirgin NAF ya gigita 'yan bindiga, mutum 20 sun tsere daga hannunsu a dajin Rugu

Katsina: Jirgin NAF ya gigita 'yan bindiga, mutum 20 sun tsere daga hannunsu a dajin Rugu

  • Jirgin saman sojoji ya kai farmaki dajin Rugu da ke Katsina inda ya tsorata wasu ‘yan bindiga
  • Hakan ya yi sanadiyyar tserewar har mutane 20 daga wadanda suka yi garkuwa da su a dajin
  • Wadanda suka samu nasarar tserewar sun bayyana cewa watannin su 5 a hannun ‘yan bindigan

Katsina - Jirgin saman sojoji wanda ya ratsa dajin Rugu a Katsina ya tsorata wasu ‘yan bindiga wanda ya yi sanadiyyar tsirar mutane 20 daga cikin wadanda suka yi garkuwa da su, ciki har da mata 10.

Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, a ranar Asabar a sansanin mahajjata wadanda suka tsira suka bayyana wa manema labarai artabun da suka yi da masu garkuwa da su wanda suka kwashe watanni 5 a hannun su.

Kara karanta wannan

Yobe: Jama'ar da jirgin NAF ya yi wa luguden wuta suna bukatar diyya

Katsina: Jirgin NAF ya gigita 'yan bindiga, mutum 20 sun tsere daga hannunsu a dajin Rugu
Katsina: Jirgin NAF ya gigita 'yan bindiga, mutum 20 sun tsere daga hannunsu a dajin Rugu. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

A cikin su akwai mata 10, mata kanana 8, wani matashi daya da kuma wani yaro, Daily Trust ta ruwaito hakan.

Rabiu Mannir, mai shekaru 27 ya ce a ranar Juma’a da dare ‘yan bindigan suka ji karar jirgin saman sojojin wanda hakan ya tsorata su suka tsere don neman tsira, hakan ya bai wa wadanda suka yi garkuwa da su damar guduwa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Muna zaune kamar kullum wasu yaran ‘yan bindiga da ke tsaron mu sai mu ka ji karar jirgin sama. Take a nan suka tsere, bayan mun ga suna gudu muka yi amfani da wannan damar wurin kwance kullin da suka yi wa kafafun mu muka tsere,” a cewarsa.

Daya daga cikin su ya kara da cewa ya sa matan suka kwashe yaran don kowa ya samu tsira.

'Yan Boko Haram sun sace tarakta 5 sun banka wa 2 wuta a Yobe

Kara karanta wannan

Masu garkuwa da mutane sun mamaye kauyen Abuja, sun sace matan aure 2

A wani labari na daban, wasu da ake zargin 'yan Boko Haram ne sun yi awon gaba da tarakta biyar tare da kone wasu biyu a Ngelbuwa da ke karamar hukumar Gujba ta jihar Yobe.

Daily Trust ta ruwaito cewa, wani mazaunin garin mai suna Kyari Konto, ya ce 'yan ta'addan sun kutsa garin inda suka dauka wani mazaunin garin wanda suka umarcesa da ya nuna musu gidajen da manoma ke da tarakta.

Shugaban wata kungiyar arewa maso gabas, reshen jihar Yobe, Nuhu Baba Hassan, ya bayyana cewa an sace taraktoci uku da suke mallakin kungiyar reshen jihar Borno da Yobe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel