Da Ɗuminsa: Ƴan acaba sun ƙwace bindigar ɗan sanda sun halaka shi da ita, sun jikkata wasu a Legas

Da Ɗuminsa: Ƴan acaba sun ƙwace bindigar ɗan sanda sun halaka shi da ita, sun jikkata wasu a Legas

  • Wasu 'yan acaba, a ranar Alhamis, 23 ga watan Satumba sun yi zanga-zanga a Legas kan abin da suka kira kwace musu babura
  • A cewar rahoton, lamarin ya faru ne a Ajao Estate a Isolo inda 'yan sanda ke kokarin kwace baburan wasu 'yan acaba
  • 'Yan acaban, wanda mafi yawancinsu 'yan arewa ne daga jihar Nasarawa suna aiki ne cikin Ajao Estate

Ajao-Estate, Legas - Wani rahoto da The Nation ta wallafa ya nuna cewa an bindige sufuritandan 'yan sanda sannan wasu 'yan sandan sun jikkata bayan 'yan acaba sun tada rikici a Legas.

Legit.ng ta tattaro cewa lamarin ya faru ne tsakanin karfe 5 zuwa 6 na yammacin ranar Alhamis, 23 ga watan Satumban 2021 a Ajao Estate a Isolo yayin da 'yan sandan ke kokarin kwace wasu babura biyar.

Kara karanta wannan

Mai shekaru 52 ya dirkawa 'yar dan uwansa mai shekaru 16 ciki har sau biyu

Da Duminsa: 'Yan acaba sun kwace bindigar dan sanda sun halaka shi, sun jikkata wasu yayin zanga-zanga a Legas
'Yan sandan Nigeria. Hoto: The Nation
Asali: Depositphotos

A cewar rahoton, 'yan sandan sun yi nasarar kwace wasu daga cikin baburan da ake ce sun saba dokokin tuki a Legas wanda hakan ya hassala 'yan acaban suka kai musu hari.

Rahoton ya nuna cewa mafi yawancin 'yan acaban da ke aiki a ciki da kewayen Ajao Estate 'yan arewa ne daga jihar Nasarawa.

An ce sun kwace bindigan sufuritandan sannan suka yi amfani da ita suka bindige shi a kan hanyar Asa Afariogun kusa da cocin RCCG.

Jaridar ta ce wani mazaunin yankin da ya nemi a boye sunansa, ya ce 'yan acaban sun kuma nufi caji ofis din don cigaba da fafatawa da 'yan sandan inda can suka raunata biyu.

Kakakin 'yan sandan jihar, Adekunle Ajisebutu, ya yi alkawarin zai bincika ya gano ainihin abin da ya faru amma bai bada bayanin ba har zuwa lokacin hada wannan rahoton.

Kara karanta wannan

Yunwa ta fara fatattakar 'yan bindiga daga jihar Katsina, inji gwamna Masari

Ya ce:

"Zan fitar da sanarwa da zarar na samu karin bayani."

PM News ta ruwaito cewa a yayin hakan, 'yan acaban da ke cikin Ajao Estate sun yi gangami sun fara kaiwa 'yan sandan hari.

'Yan acaban sun yi taron dangi sun ci galaba kan sufetan 'yan sandan sun kwace bindigarsa kuma suka halaka shi da ita.

Karin Bayani: Bincike ya nuna abinda ya kashe budurwar da aka tsinci gawarta cikin motar basarake da ya tsere

A wani labarin daban, binciken da aka gudanar a kan gawar wata budurwa, Faith Aigbe mai shekaru 26 da aka tsinta a cikin motar basarake na jihar Edo ya nuna cewa ta rasu ne sakamakon juna biyu mai matsala da ta ke dauke da shi, rahoton LIB.

Idan za a iya tunawa dai, an zargi Enogie na Uroho a karamar hukumar Okha na jihar Edo, Iguodala Ogieriakhi da yi wa Faith duka har ya kashe ta bayan tsintar gawarta a motarsa Lexus 330 da ya tsere ya bari a harabar asibiti kamar yadda Legit Hausa ta kawo a baya.

Kara karanta wannan

Sojoji sun hallaka kasurguman yan bindiga 5, tare da mabiyansu 23 a Zamfara

Amma, basaraken ya musanta zargin, yana mai cewa Faith tana dauke da juna biyu ne na watanni takwas kuma ta rasu ne a lokacin da ta ke kokarin zubar da cikin.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel