Zamu yi amfani da miƙa wuyan mayaƙan Boko Haram mu dawo da zaman lafiya a Arewa da Izinin Allah, Zulum

Zamu yi amfani da miƙa wuyan mayaƙan Boko Haram mu dawo da zaman lafiya a Arewa da Izinin Allah, Zulum

  • Gwamnan Borno, Farfesa Zulum, yace gwamnatinsa tare da haɗin guiwar FG zasu yi amfani da miƙa wuyan Boko Haram domin dawo da zaman lafiya
  • Gwamnan yace matakin da mayakan Boko Haram suka ɗauka na aje makamansu cigaba ne mai kyau da ake bukata
  • Zulum ya bayyana cewa tun watan Fabrairu al'ummar jihar Borno suke rayuwa ba tare da hasken wutar lantarki ba

Borno - Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umaru Zulum, yace gwamnatinsa zata haɗa kai da FG wajen amfani da miƙa wuyan yan Boko Haram domin dawo da zaman lafiya a yankin arewa maso gabas.

Gwamnan yace matakin da yan ta'addda suka ɗauka cigaba ne mai kyau kuma gwamnati ta ɗauki mataki watanni biyu da suka wuce na tallafawa miƙa wuyan yan Boko Haram da kuma dawo da zaman lafiya.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Zulum ta fara shiri na musamman kan mayakan Boko Haram da suka mika wuya

Vanguard ta rahoto cewa Zulum ya faɗi haka ne a wurin taron da ma'aikatar yaɗa labarai ta shirya ranar Alhamis, kan kayan gwamnati da aka lalata kamar hanyoyin sadarwa da wutar lantarki a Borno.

Gwamnan Borno, Farfesa Babagana Zulum
Zamu yi amfani da miƙa wuyan mayaƙan Boko Haram mu dawo da zaman lafiya a Arewa da Izinin Allah, Zulum Hoto: The Governor of Borno State FB Fage
Asali: Facebook

Mun ɗauki mataki tun a baya - Zulum

Gwamna Zulum yace:

"Miƙa wuyan da mayaƙan Boko Haram suke cigaba da yi, abu ne mai kyau da muke bukata. Wata biyu da suka wuce, mun ɗauki matakin amfani da wannan damar."
"Zuwa yanzun, dubbanninsu sun miƙa wuya, muna samun cikakken goyon baya daga rundunar sojoji, yan sanda, jami'an farin kaya DSS, da sauransu wajen tabbatar da cimma nasara a lamarin."
"Gwamnatin Borno da FG suna aiki tare domin samar da hanyoyin da zasu taimaka wajen samun nasara, kuma shugaban ƙasa ya yi alƙawarin bada duk gudummuwar da ya kamata."

Kara karanta wannan

Kada ku tausayawa yan bindiga, ku buɗe musu wuta koda sun shiga cikin mutane, Gwamnan Arewa ya hasala

Game da lalata kayayyakin gwamnati

Game da lalata manyan kayayyakin gwamnati, Farfesa Zulum, yace mutanen Borno sun jima suna rayuwa cikin duhu.

Gwamnan yace tun watan Fabrairu lokacin da miyagun yan Boko Haram suka lalata hanyoyin sadarwa da wutar lantarki, mutane suke rayuwa cikin duhu.

A wani labarin na daban kuma, Jam'iyyar APC ta bayyana dalilin da yasa ta dage gangamin taronta na jihohi

Jam'iyya mai mulkin ƙsar nan APC, ta bayyana cewa ta ɗauki matakin ɗage gangamin jihohi ne saboda bikin ranar samun yancin kai.

APC tace ranar da ta saka da farko, ta kasance kwana ɗaya tal bayan ranar bikin samun yankin kai, kuma mambobinta zasu halarci bikin a jihohinsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Tags: