Karya ake yi, ba mu ce mun yi nadamar zaben Buhari a 2015 ba inji Kungiyar Dattawan Arewa

Karya ake yi, ba mu ce mun yi nadamar zaben Buhari a 2015 ba inji Kungiyar Dattawan Arewa

  • Kungiyar dattawan Arewacin Najeriya ba ta yi nadamar zabin ta a zaben 2015 ba
  • Kakakin NEF na kasa, Hakeem Baba-Ahmed ya musanya rade-radin da ke yawo
  • Dr. Baba-Ahmed yace babu wani da-na-sanin zaben Buhari a maimakon Jonathan

Nigeria - Kungiyar dattawan Arewacin Najeriya watau NEF, ta fito ta bayyana cewa babu wani shafa keya da take yi a kan zaben Muhammadu Buhari.

Mai magana da yawun bankin kungiyar NEF, Dr. Hakeem Baba-Ahmed, ya yi magana a shafin Facebook, yace rade-radin da ke yawo ba gaskiya ba ne.

Da yake karin-haske a ranar Laraba, 22 ga watan Satumba, 2021, dattijon yace babu inda ya fada wa wani cewa suna nadamar ba Buhari kuri’unsu a 2015.

Hakeem Baba-Ahmed ya zargi mutane da murguda kalamansa, yace a hirar da aka yi da shi, babu inda yace Arewa tana nadamar kada wa APC kuri’arta.

Kara karanta wannan

Kungiyar Musulunci ta bayyana boyayyar hikimar jawo Fani-Kayode cikin Jam’iyyar APC

Jaridun kudu sun yi karya?

“Wasu jaridu suna yada karya cewa kungiyar dattawan Arewa tace tayi da-na-sanin zaben Muhammadu Buhari a kan Goodluck Jonathan a 2015.”
“Mun yi fatan ina ma shugaba Buhari ya cin ma abin da aka sa rai zai aiwatar, amma ban taba cewa mun yi nadamar mara masa baya a 2015 ba.”
Hakeem Baba Ahmad
Kakakin Kungiyar NEF, Dr. Hakeem Baba Ahmad Hoto: dailytrust.com
Asali: Twitter

“ Da gangan ake yada wadannan karyayyaki domin a bata wa kungiyar nan (ta NEF) suna.”
“Na wallafa cikakkiyar hirar da aka yi da ni, inda aka tabo wannan batun a kan shafina.”

Matasa suna da-na-sani kuwa?

Shi kuma wani Bawan Allah mai suna Ahmad Rufai Isa, ya maida wa Baba-Ahmed martani a shafinsa, yace idan dattawa ba su yi da-na-sani ba, su suna yi.

“Idan ku dattawa ba kuyi nadamar zabarsaba to mu talakawa da muke ji ajikinmu, munyi nadamar. A cikinta ma muke ehe.

Kara karanta wannan

Mun yi nadamar yakar Jonathan don Buhari yaci zabe, Dattawan Arewa

“Allah (SWT) ya bamu ikon cin wannan jarabawar. Allah ya kawo mana shugabanni nagari wadanda zasu tausaya mana.”

Idan za ku tuna, da aka yi hira da Hakeem Baba-Ahmed a makon nan, yace yana ganin akwai bukatar a samu shugaban kasan da ya karbu a Kudu da Arewa.

Da yake bayani a gidan talabijin, Hakeem Baba-Ahmed yace Arewa ta shiga matsala a yau ne saboda idan ya rufe a kan daga wani yanki shugaban kasa zai fito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel