Mun yi nadamar yakar Jonathan don Buhari yaci zabe, Dattawan Arewa

Mun yi nadamar yakar Jonathan don Buhari yaci zabe, Dattawan Arewa

  • Shugaba Buhari ya kunyata miliyoyin yan Najeriya har da yan a mutun APC, Baba Ahmed
  • Kaakin Dattawan Arewa yace sun yi nadamar kawar da Jonathan a 2015
  • Ya yi kira ga jama'a su san irin wanda zasu zaba a 2023

Kungiyar dattawan Arewa ta bayyana cewa ta yi nadamar yaki da tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, don ganin cewa Shugaba Buhari ya ci zabe a shekarar 2015.

Kungiyar ta yi Alla-wadai da yadda Buhari ya kunyata miliyoyin yan Najeriya har da 'yayan jam'iyyarsa ta All Progressives Congress da suka yi aiki tukuru don ganin ya ci zabe.

Saboda haka, kungiyar dattawan Arewan ta ce Shugaban kasan da za'a yi nan gaba ya kasance mutum wanda zai bi tafarki irin na Buhari ba.

Kara karanta wannan

Yadda za a fito da Magajin Shugaba Buhari, mun koyi hankali yanzu inji Dattawan Arewa

Kakakin kungiyar, Dr. Hakeem Baba-Ahmed, yayi wannan jawabi a hirarsa da yan jarida a shirin ‘The Morning Show’ na tashar Arise TV ranar Talata.

A cewarsa:

"Shin akwai wani dan Najeriyan da Shugaba Buhari bai ba kunya ba yanzu, har da yan a mutun APC? Shin akwai wanda zai ce Buhari bai gaza ba?"

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Mun yi masa kyakkyawan zato, mun fadawa mutane, 'Kuyi watsi da Jonathan, ku zabi Buhari, zai yi yaki da rashawa, zai magance matsalar tsaro, zai gyara tattalin arziki' amma kalli inda muke yanzu."

Mun yi nadamar yakar Jonathan don Buhari yaci zabe
Mun yi nadamar yakar Jonathan don Buhari yaci zabe, Dattawan Arewa Hoto: Channels TV
Asali: UGC

Yadda za a fito da Magajin Shugaba Buhari, mun koyi hankali yanzu

Dattawan Arewa sun yi magana kan yadda za a bi a fito da sabon shugaban kasa yayinda wa’adin shugaba mai-ci Muhammadu Buhari zai kare a 2023

Da yake magana a ranar Talata, 21 ga watan Satumba, 2021, Dr. Hakeem Baba Ahmed ya sake jaddada ra’ayinsa na cewa ba za a bar Arewa a baya ba.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun yi ram da gurgu mai shekaru 22 kan zargin garkuwa da mutane

Hakeem Baba Ahmed yace ya kamata a samu shugaban kasan da zai tafi da kowa da kowa, a maimakon a ce zai wakilci bangarensa.

Yace:

“A siyasa babu abin da ke da tasiri irin yawan kuri’u. Mutane suna ja da karfin kuri’un Arewa, da adadin mutanen yankin, su duba zabukan da aka yi a da.”
“Ba yana nufin kowane ‘dan Arewa zai zabi ‘dan takarar Arewa ne ba. Tarihi ya nuna miliyoyin 'yan Arewa sun zabi ‘yan takaran kudancin Najeriya.”

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng