Yadda za a fito da Magajin Shugaba Buhari, mun koyi hankali yanzu inji Dattawan Arewa

Yadda za a fito da Magajin Shugaba Buhari, mun koyi hankali yanzu inji Dattawan Arewa

  • Kungiyar dattawan Arewa ta fadi abin da ya dace a samu a shugaban kasa a 2023
  • Dr. Hakeem Baba-Ahmed yace ba za a bude wa Arewa ido cewa su bada mulki ba
  • Dattijon yana ganin akwai bukatar a samu shugaban kasan da zai karbu a ko ina

Abuja - Dattawan Arewa sun yi magana kan yadda za a bi a fito da sabon shugaban kasa. Wa’adin shugaba mai-ci Muhammadu Buhari zai kare a 2023.

Jaridar Daily Trust tace kakakin kungiyar dattawan Arewa (NEF), Dr. Hakeem Baba Ahmed ne ya yi wannan bayani da aka yi hira da shi a gidan talabijin.

Da yake magana a ranar Talata, 21 ga watan Satumba, 2021, Dr. Hakeem Baba Ahmed ya sake jaddada ra’ayinsa na cewa ba za a bar Arewa a baya ba.

Kara karanta wannan

Gwamnan Kano Ganduje ya yi magana a game da wanda zai gaji kujerarsa a 2023

Hakeem Baba Ahmed ya fada wa Arise TV cewa ya kamata a samu shugaban kasan da zai tafi da kowa da kowa, a maimakon a ce zai wakilci bangarensa.

Kowa yana bukatar kowa a siyasa

“A siyasa babu abin da ke da tasiri irin yawan kuri’u. Mutane suna ja da karfin kuri’un Arewa, da adadin mutanen yankin, su duba zabukan da aka yi a da.”

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Ba yana nufin kowane ‘dan Arewa zai zabi ‘dan takarar Arewa ne ba. Tarihi ya nuna miliyoyin 'yan Arewa sun zabi ‘yan takaran kudancin Najeriya.”
Kakakin NEF
Dr. Hakeem Baba Ahmed Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Haka zalika mutanen yankin Kudu su kan zabi ‘yan siyasan da suka fito daga Arewa a zabe. Baba-Ahmed yace kowane yanki na bukatar ‘danuwansa a zabe.

Dole shugaban kasa ya fito daga Kudu?

“Abin da muke cewa shi ne babu wanda ya isa ya yi mana barazana. Mun karanta tsarin mulki, mun san me ake bukata wajen zama shugaban kasa.”

Kara karanta wannan

Jonathan zai yi caca idan ya bar PDP saboda ya samu tikitin 2023 inji Kungiyar Gwamnonin APC

“Mun san dole a zo lokacin da mutumin kudu zai zama shugaban kasa, kuma dole hakan za a yi. Amma sai ya kasance mai farin jini ne a Kudu da Arewa.”
“Dole ne ya zama shugaban kasar Najeriya, ba na wata kabila, ko na wani addini, ko wani yanki ba. Mun yi hankali da cewa dole sai namu zai yi mulki.”

Dattijon yace Arewa tana cikin matsala a yau ne saboda na taya jefa ta a ha’ula’i. Baba-Ahmed yace ya kamata a daina maganar daga ina shugaban kasa ya fito.

Siyasar Kano sai Kano

A Kano kuma mun ji gwamna Abdullahi Ganduje ya yi maganar da ta saba ta mai dakinsa. Gwamnan yace batun cewa ina da ‘Dan takara a 2023 karya ne.

A jiyan ne kuma aka ji cewa babba jami'in NNPC na kasa, Inuwa Waya ya ajiye aikinsa. Ana tunani Waya zai nemi tikitin Gwamnan jihar Kano a APC ne a 2023.

Kara karanta wannan

Batun yankin da za a ba tikitin Shugaban kasa a 2023 ya raba kan wasu Gwamnonin PDP

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng