Kungiyar Musulunci ta bayyana boyayyar hikimar jawo Fani-Kayode cikin Jam’iyyar APC
- Muslim Rights Concern ta yabi Cif Femi Fani-Kayode da ya dawo APC
- Kungiyar MURIC tace sauya-shekar ‘dan siyasar za ta amfani mutane
- Farfesa Ishaq Akintola yake cewa ‘dan siyasar ya yi koyi da mahaifinsa
Nigeria - Kungiyar Muslim Rights Concern (MURIC), tace mutanan Najeriya za su amfana da sauya-shekar da Femi Fani-Kayode ya yi zuwa jam’iyyar APC.
Shugaban kungiyar ta MURIC, Farfesa Ishaq Akintola ya fitar da jawabi a ranar Lahadi, yace ba za su shiga sahun sauran masu sukar sauya-shekan ‘dan siyasar ba.
Jaridar Vanguard ta rahoto Ishaq Akintola yana cewa akwai yiwuwar Femi Fani-Kayode ya sauka daga ra’ayoyin da yake a kai tun da ya shigo jam’iyya mai mulki.
“Fani-Kayode mutum ne wanda baro-baro yake goyon bayan masu kiran a barka kasa. Ana neman jawo yaki saboda aika-aikan wadanda yake mara wa baya.”
“A yau duk ta kare Fani-Kayode zai koma kiran a hada-kai a Najeriya a inda ya samu kansa.”
“A kan wannan ne muke yaba wa abin da mahaifin FFK, Remi Ade Fani Kayode ya yi a shekarun 1970s, ya ajiye siyasar kabilanci, ya hada-kai da Arewa.”
MURIC take cewa Cif Remi Ade Fani Kayode ya yi hakan ne domin a samun hadin-kai a kasar.
A cewar kungiyar, a yau ‘dansa Femi Fani Kayode ya yi irin abin da tsohonsa ya yi a Najeriya. Yace ya kamata sauya-shekar da FFK ya yi ya fara daga zuciyarsa.
"Dole mu manta da cewa ya yi wa kowa kaca-kaca (har da shugaban MURIC) saboda sabanin fahimta, a yau sai a yaba masa na irin dattakun da ya nuna.”
A karshe Farfesa Ishaq Akintola ya yaba wa shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya manta da abin da FFK ya yi masa a baya, ya karbe shi hannu biyu a APC.
Obasanjo ya zama Jakadan zaman lafiya
Kwanakin baya aka ji labari cewa kungiyar AU ta ba Olusegun Obasanjo nauyin kawo zaman lafiya a Somaliya, Kenya, Sudan, da wasu kasashen Afrika ta gabas.
Olusegun Obasanjo ya fara karada kasashen domin kawo zaman lafiya da kwanciyar hankali.
Asali: Legit.ng