Kawancen shekaru 80: Inyamura ta taya kawarta Bahaushiya murnar cika shekaru 90

Kawancen shekaru 80: Inyamura ta taya kawarta Bahaushiya murnar cika shekaru 90

  • Kawaye biyu da suka kasance tare tsawon shekaru 80 sun burge zukata a shafukan sada zumunta yayin da ɗayansu ke murnar cika shekaru 90
  • An yada wani bidiyo na matan a shafukan sadarwa inda suka yi kyau matuka cikin shiga iri daya
  • Mai bikin ta fito ne daga Maiduguri yayin da kawarta ta fito daga kudu maso gabas; ita ma za ta cika shekaru 90 a watan Disamba

Bidiyon wasu mata 'yan Najeriya biyu da suka kasance kawaye tsawon shekaru 80 sun burge zukata a kafafen sada zumunta yayin da ɗayansu ke murnar cika shekaru 90 a duniya.

A cikin bidiyon da @lindaikejiblogofficial ta wallafa a shafin Instagram, an yi wa matan ado da riguna launin shuɗi don bikin zagayowar ranar haihuwar daya daga cikinsu.

Kawancen shekaru 80: Inyamura ta taya kawarta Bahaushiya murnar cika shekaru 90
Kawancen shekaru 80: Inyamura ta taya kawarta Bahaushiya murnar cika shekaru 90 Hoto: @lindaikejiblogofficial
Asali: Instagram

Mai bikin ta fito ne daga Maiduguri yayin da kawarta ta fito daga kudu maso gabas; ita ma za ta cika shekaru 90 a watan Disamba.

Kara karanta wannan

'Yan fashin daji ne ke kewaye da mu, Al'ummar Kaduna sun koka

A cewar mutumin da ke daukar bidiyon, kasancewar matan biyu ba 'yan kabila daya ba kuma suna gudanar da addinai daban -daban yana nufin akwai lokacin da abubuwa za su inganta a Najeriya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Mutumin ya yi wa matan addu’a kuma ya ce yana fatan kasancewa a wurin lokacin da za su yi bikin cika shekaru 100 da haihuwa.

Bidiyon ya burge zukata

'Yan Najeriya a shafukan sada zumunta sun burge kuma ba da dadewa ba suka mamaye sashin sharhi don bayyana ra'ayinsu akan hakan.

@daddyshowkey ya ce:

"Shin har yanzu muna da wannan a Najeriya."

@_mz_boomie ya rubuta:

"Har sun ma fara kama da juna.”

@vitaminkitchenng yayi sharhi:

"Waɗannan sun zama 'yan'uwan juna, aminai."

@spacesbybloom ya ce:

"Kai ... Wataƙila shi ya sa suka daɗe haka ... Idan baku da kishi, hassada da ƙiyayya a cikin ku .. barka da zagayowar ranar haihuwa ga waɗannan kyawawan rayuka."

Kara karanta wannan

Kaduna: Hotunan 'yan sanda masu murabus suna yi wa hukumar fansho zanga-zanga

Ban taba son yarana su yi kama da ni a domin ba na da kyau: Jarumin fim ya magantu

A wani labari na daban, fitaccen jarumin wasan kwaikwayo na Nollywood, John Okafor wanda aka fi sani da Mista Ibu, kwanan nan yayi magana ta gaskiya game da kamanninsa da kuma yadda baya son yaransa su bi sahun shi.

Da yake magana yayin wata hira da aka yi da shi kwanan nan a wani faifan bidiyo da Goldmyne TV ya sanya a shafin Instagram, tauraron fim din ya yarda cewa lokacin da ya haifi dansa na farko a 1991, ya roki Allah kan kada Ya sa jaririnsa ya yi kama da shi.

A cewarsa, ya kasance mai farin ciki da godiya ga Allah saboda haihuwar dansa amma yana son ya yi kama da mahaifiyarsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel