Sirrin fararen Hakora: Hanyoyi 8 da za ku bi domin sanya Hakoranku suna sheki

Sirrin fararen Hakora: Hanyoyi 8 da za ku bi domin sanya Hakoranku suna sheki

- Fararen hokara na kara kwarin gwuiwar magana a cikin abokai ba tare da jin kunya ba

- Yawancin mutane ba su da masaniyar yadda zasu magance matsalar rashin fararen hakora wasu har suna zaton halitta ne, to ga haya mai sauki a cikin rahotan da Legit.ng ta kawo muku

Kamar yadda kowane sashi na jikin dan Adam yake bukatar kulawa, haka zalika Hakora ma na bukatar kulawar mai su. A yau Legit.ng ta shiryo muku ta bayyana hanyoyin da za’a bi cikin sauki don samun lafiyayyun hakora masu haske da sheik har ma su rika walkiya. Hanyoyi sune kamar haka:

Dabi’ar cin abinci

Sirrin farin Hakori: Hanyoyi 8 da za ku bi domin sanya Hakoranku suna sheki
Sirrin farin Hakori: Hanyoyi 8 da za ku bi domin sanya Hakoranku suna sheki

Da farko dai sun bayyana cewa dole mutum ya canja dabi’arsa ta cin abinci, ma’ana mutum ya kasance yana cin abubuwa mai gina jiki, kuma yana da kyau ya gujewa cin abincin da yake da tarin sukari a cikinsa (Sugar). Ta’ammali da abubuwan da suka da hada Madara, Nono da kuma shan wadaccen ruwa mai tsafta da sauransu yana inganta lafiyar Hakori

Amfani da Danko (Chewing Gum)

Sirrin farin Hakori: Hanyoyi 8 da za ku bi domin sanya Hakoranku suna sheki
Sirrin farin Hakori: Hanyoyi 8 da za ku bi domin sanya Hakoranku suna sheki

Taunar Danko wato wanda aka fi sani da Chewing gum a turance yana taimakawa matuka gaya wajen hana zaman wani abu a cikin sakon hakori, a sanadaiyyar hakan ka iya jawo tsutsar hakori dama sauran dangogin matsalolin da suka shafi hakorin baki daya.

Amfani tare da sauya magogin baki (Toothbrush)

Sirrin farin Hakori: Hanyoyi 8 da za ku bi domin sanya Hakoranku suna sheki
Sirrin farin Hakori: Hanyoyi 8 da za ku bi domin sanya Hakoranku suna sheki

Yana da matukar muhimmanci, wanke baki akai-akai domin yin hakan zai taimaka wajen wanke tare da fitar da duk wani nau’in abun da ya makale a hakorin. Haka zalika yana da kyau ace mutum yana sauya magogin bakinsa duk tsawon wani lokaci (a kalla duk bayan wata uku). Bayan amfani da magogin baki yana da kyau ace an wanke da ruwa mai tsafta sannan a barsa ya bushe tare da samar masa wajen ajiya mai kyau, amma kar ya zama ana barinsa a bayan gida (Toilet) kamar yadda wasu suka maida dabi’arsu, wanda hakan ka iya jawo wasu kwayoyin cututtuka su hau kan shi magogin bakin.

Kulawa ta musamman ga hakora

Sirrin farin Hakori: Hanyoyi 8 da za ku bi domin sanya Hakoranku suna sheki
Sirrin farin Hakori: Hanyoyi 8 da za ku bi domin sanya Hakoranku suna sheki

Kungiyar kula da lafiyar hakora ta duniya wato International Dental Health Association, ta bayyana cewa kaso 42% ne na mutane ke amfani da magogin baki domin kula da lafiyar hakori. Sun sake jero wasu hanyoyin da suke ganin yin su zai taimaka gaya wajen samuwar ingantattun hakora;

Wanke baki da magogi har na tsawon mintuna biyu (2 Minutes) akalla sau biyu a rana.

Kuskure baki da ruwa lokaci zuwa lokaci, musamman bayan kamala cin abinci ko wani abu mai dauke da abun da zai iya zama a hakori.

Amfani da maganin wanke baki wanda da dama daga cikinsu suna dauke da sinadarin kariya (Antibacterial) wanda yana taimakawa wajen wanke duk wani abu tare da karawa hakora kwari.

Ganin Likitan Hakori

ziyara ga likitan Hakori yana da matukar amfani, saboda yin hakan zai taimaka wajen duba da irin halin da hakoran ke ciki, sannan in har akwai wani abu da yake damun hakoran, likitan zai iya bada shawara ko magani domin kauda cutar tun kafin ta zama babba. Likitan zai iya yin wankin Hakori wanda hakan zai bawa mai su damar jin dadi sosai, kuma yana da kyau ake yin wanki hakori akalla sau daya a shekara.

KU KARANTA: IBB ya mika kokon bara ga 'yan Najeriya dangane da zaben 2019

Karin amfani da sinadarin Vitamin

Kamar yadda bayanai suka gabata cewa, a kaucewa cin abubuwa masu sukari da yawa, a nan kuma an bayyana cewa amfani da abinda yake dauke da sinadarin Vitamin zai taimaka sosai. Cin abinci mai dauke da ganyayyaki kamar su kabeji, Salak, lansir,Zogale da sauran Ganye yana da amfani. Cin kayan itatuwa kamar lemo, Ayaba, Kankana, Inibi duk suna da fa’ida sosai wajen lafiyar hakori. Har wayau, cin abinda ya shafi nau’in abinda ke cikin ruwa kamar su Kifi, da sauransu wanda duk suna dauke da nau’in Vitamin D zasu taimaka gaya.

Amfani da Man Kwakwa

Sirrin farin Hakori: Hanyoyi 8 da za ku bi domin sanya Hakoranku suna sheki
Sirrin farin Hakori: Hanyoyi 8 da za ku bi domin sanya Hakoranku suna sheki

Mutum zai iya amfani man kwakwa wajen wanke baki. Cokali daya na man kwakwa mutum zai diba ya wanke bakinsa har na tsawon mintuna 20 har sai yawun bakin mutum da man kwakwar sun canja launi zuwa launin madara, sannan a zubar amma fa kar a hadiye.

Mutum zai iya hada man wanke baki da kansa Makilin (toothpaste)

Sirrin farin Hakori: Hanyoyi 8 da za ku bi domin sanya Hakoranku suna sheki
Sirrin farin Hakori: Hanyoyi 8 da za ku bi domin sanya Hakoranku suna sheki

Akwai abubuwa da akan yi amfani da su domin hada abun wanke baki, wannan abubuwa su ne kamar haka:

Cokali 4 na hodar Calcium

Cokali 1 na Stevia

Cokali 1 na Gishiri (salt)

Cokali 2 na Baking Soda

Kaso ¼ na kofin man kwakwa

Wadannan su ne jerin hanyoyin da in kunyi amfani da su zasu taimaka wajen kara tsaftar hakori tare da kara musu inganci.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku

ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel