Jerin manyan yan adawan gwamnatin Buhari 4 da suka mutu a shekarar nan

Jerin manyan yan adawan gwamnatin Buhari 4 da suka mutu a shekarar nan

Daga farkon shekarar nan kawo yanzu, Najeriya ta yi rashin yan fafutuka hudu da suka shahara da adawa da gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari.

Wadannan mutane sun kwashe karshen rayuwansu suna kira ga shugaban kasan da gwamnatinsa su tashi tsaye kan halin da yan Najeriya ke ciki.

Legit ta tattaro muku jein mutum hudu kamar yadda Sahara Reporters ta koro:

1. Marigayi Dr. Junaid Mohammed

Dr. Junaid Mohammed, ya rasu ne ranar 18 ga Febrairu, 2021.

Junaid, wanda kwararren Likita ne ya kasance dan fafutuka kuma mai sharhi kan lamuran yau da kullum.

A 2015, ya zargi Shugaba Buhari da nuna kabilanci da son kai wajen nade-nade a gwamnatinsa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yana daya daga cikin wadanda suka zargi 'dan uwan Buhari, Mamman Daura, da zama masu juya mulkin Najeriya madadin Buhari.

Kara karanta wannan

Hotunan shugaba Buhari yayin da yake hawa jirgi zuwa kasar Amurka

2. Yinka Odumakin

Ranar 13 ga Afrilu, shahrarre dan fafutuka kuma Kakakin kungiyar kare hakkin Yarabawa, Yinka Odumakin ya mutu.

Odumakin ya kasance babban dan adawan gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari.

Gabanin mutuwar da yayi sakamakon cutar COVID-19, Odumakin ya caccaki gwamnatin Buhari kan yunkurin kama mai rajin kafa kasar Oduduwa, Sunday Igboho.

Yan makonni bayan mutuwarsa hukumar DSS ta kai simame gidan Igboho dake Soka, Ibadan, jihar Oyo.

Jerin manyan yan adawan gwamnatin Buhari 4 da suka mutu a shekarar nan
Jerin manyan yan adawan gwamnatin Buhari 4 da suka mutu a shekarar nan Hoto: SR
Asali: Facebook

3. Barr Olusegun Bamgbose

Barista Olusegun Bamgbose wanda shine shugaban kungiyar masu kira ga shugabanci na kwarai (CAGG) ya mutu ranar 18 ga Satumba, 2021.

Daga cikin jawaban da ya saki ana saura yan kwanaki da mutuwarsa, ya yi kira ga Buhari ya daina barci ya tashi tsaye don magance matsalar tsaron da ta addabi Najeriya.

Lauyan yayi wannan jawabi ne biyo bayan harin da yan bindiga suka kai makarantar Soji NDA dake jihar Kaduna inda suka kashe Soji 2 kuma sukayi garkuwa da 1.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Me niyyar takarar kujerar shugaban kasa a 2023 ya mutu

4. Obadiah Mailafiya

Tsohon mataimakin gwamnan babban bankin Najeriya, Obadiah Mailafiya, ya mutu ne ranar Asabar, a asibitin koyarwan jami'ar Abuja dake Gwagwalada.

Mailafiya wanda yayi takara da Buhari a zaben shugaban kasan 2019 karkashin jam'iyyar ADC ya shahara da caccakan gwamnatin Buhari.

Asali: Legit.ng

Online view pixel