Mayakan Boko Haram da Suka Mika Wuya Sun Yi Dana Sanin Daukar Makamai, Sun Fadi Dalilinsu

Mayakan Boko Haram da Suka Mika Wuya Sun Yi Dana Sanin Daukar Makamai, Sun Fadi Dalilinsu

  • Mayakan Boko Haram da suka miƙa wuya ga rundunar soji sun nuna dana sani kan aikin da suka yi a baya
  • Tubabbun yan Boko Haram ɗin sun kuma yi kira ga ragowar yan ta'adda dake cikin daji, su fito domin aje makamansu
  • Rundunar sojoji ta bayyana cewa dubbannin yan ta'adda sun miƙa wuya ga jami'anta tun daga watan Yuli

Borno - Wasu daga cikin mayakan Boko Haram da suka mika wuya ga sojoji sun yi dana sanin ɗaukar makami, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Tubabbun yan ta'addan sun bayyana haka ne yayin da manema labarai suka kai ziyara ɗaya daga cikin wuraren da ake tantance masu miƙa wuya a Borno ranar Talata.

Ɗaya daga cikin mayaƙan da suka mika wuya yace kwamndojinsu sun yaudare su kan dalilin da yasa suka ɗauke su aiki.

Kara karanta wannan

Ina tabbatar muku za'a hukunta tubabbun yan Boko Haram: Kwamandan Operation Hadin kai

Mayakan Boko Haram da Suka Mika Wuya
Mayakan Boko Haram da Suka Mika Wuya Sun Yi Dana Sanin Daukar Makamai, Sun Fadi Dalilinsu Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Ya ƙara da cewa shi da waɗanda suka miƙa wuya sun fahimci cewa ba zai yuwu su cigaba da zama a jeji ba suna yaƙi da jami'an tsaro.

Meya hana yan ta'addan miƙa wuya tun a baya?

Mutumin yace sun so aje makaman su tun a baya amma suna tsoron jami'an tsaro su damƙe su, sannan su kashe su, kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

A cewarsa miƙa wuyan da suka yi a yanzu shine abinda ya dace, kuma ya yi kira ga ragowar yan ta'addan su aje makamansu.

Yace:

"Mun ji tsoron za'a kashe mu idan muka fito miƙa wuya amma abun ba haka yake ba, an karɓe mu ba tare da an mana komai ba."
"Ina kira ga ragowar yan ta'adda dake cikin daji, su gaggauta fitowa don mika wuya, domin za'a karɓe su."

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba da Matar Aure Mai Shayarwa da Wani Ɗan Kasuwa a Jalingo

Kwamandan runduna ta musamman 21, Birgediya Janar Adewale Adekeye, yace dubbannin mayakan Boko Haram sun miƙa wuya tun watan Yuli.

A wani labarin kuma Shugaba Buhari ya aike da wasika ga majalisar dattijai, ya bukaci yin garambawul a PIA

A wasikar da ya aike wa sanatocin ranar Talata, Buhari ya nemi majalisar ta zare ministoci biyu daga mambobin kwamitin zartarwa na NNPC.

Hakazalika shugaban ya bukaci sanatocin su tantance mambobin majalisar zartarwa ta hukumar EFCC, mai yaƙi da cin hanci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Tags: