Tura ta kai bango: Fusatattun matasa sun kai samame maɓuyar masu garkuwa, sun cinna musu wuta da ransu

Tura ta kai bango: Fusatattun matasa sun kai samame maɓuyar masu garkuwa, sun cinna musu wuta da ransu

  • Fusatattun matasa da ke anguwar Isoko a jihar Delta sun banka wa wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne wuta bayan ‘yan bindigan sun halaka mutane 2
  • An samu bayanai akan yadda lamarin ya faru bayan ‘yan sa kai sun bi sawun ‘yan bindigan har suka gano maboyar su dake dajika
  • Matasan sun je har ofishin ‘yan sandan da ‘yan sa kai su ka kai su dauke da adduna da bindigogin toka sannan suka kona ‘yan bindigan 6

Jihar Delta - Fusatattun matasa sun samu nasarar halaka wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne da su ka yi garkuwa da mutane 2 kuma su ka halaka su a anguwar Isoko da ke jihar Delta.

The Punch ta tattaro bayanai akan yadda lamarin ya faru bayan rundunar ‘yan sa kan yankin sun bi sawun ‘yan bindigan har suka gano sansanin su da ke daji.

Kara karanta wannan

Adamawa: ‘Yan sanda sun kama mutum 21 da ake zargin sun halaka mutum 7 da tsafi

Tura ta kai bango: Fusatattun matasa sun kai samame maɓuyar masu garkuwa, sun cinna musu wuta da ransu
Taswirar Jihar Delta: Hoto: Vangaurd NGR
Asali: Twitter

Sun samu nasarar babbaka ‘yan bindiga shida

Sakamakon turnukun, fusatattun matasan sun samu nasarar halaka ‘yan bindiga shida.

The Punch ta kara gano yadda ‘yan sakan yankin dauke da adda da bindigogin toka suka hada kai da ‘yan sandan wurin binciko su.

Kamar yadda wata majiya ta bayyana, ‘yan sa kan sun kai ‘yan bindigan har ofishin ‘yan sanda.

Matasan sun kutsa ne har ofishin ‘yan sandan sannan su ka kwaso su suka babbaka su

Saidai fusatattun matasan sun nufi ofishin ‘yan sandan inda suka kutsa suka kama wadanda ake zargin ‘yan bindiga ne kuma suka banka musu wuta.

Bayan neman jin ta bakin jami’in hulda da jama’an rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Bright Edafe ya ce bai san komai ba dangane da faruwar lamarin har lokacin da ake rubuta rahoto.

Kara karanta wannan

‘Yan bindigan da aka fatattako daga Zamfara sun tare hanyoyin Katsina suna neman abinci

Adamawa: Jarumin mai shago ya ragargaji ‘yan daba 2 da su ka yi kokarin fasa masa shago

A wani rahoton, kun ji wani mai shago, Mohammed Hamman Adama, ya nuna gwarzontakarsa bayan ya yi dambe da wasu yaran Shila yayin da su ka yi kokarin balle masa shagon sa da ke Sangere Bode a karamar hukumar Yola ta kudu a jihar Adamawa.

LIB ta ruwaito yadda aka tattaro bayanai akan wadanda ake zargin, Umar Sa’ad, mai shekaru 18 da Mohammed Idris, mai shekaru 20 suka lallaba shagon sa da misalin karfe 2:00 na daren 2 ga watan Satumban 2021 da addunan su, gudumomi, sanduna da sauran miyagun makamai.

Bayan isar su shagon har sun fara balle kofar don su samu nasarar yasar shagon. Su na kici-kicin balle kofa mai shagon ya ji kara ya fita cikin sauri.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Tags: