Adamawa: ‘Yan sanda sun kama mutum 21 da ake zargin sun halaka mutum 7 da tsafi

Adamawa: ‘Yan sanda sun kama mutum 21 da ake zargin sun halaka mutum 7 da tsafi

  • ‘Yan sanda sun kama mutane 21 da ake zargin su na da hannu a tsafin da ya halaka mutane 7 a wani kauye dake jihar Adamawa
  • Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Aliyu Adamu ya bayyana hakan a wani taron manema labarai ranar Litinin a yola inda ya ce Dukan su ‘yan kauyen Dasin Bwate ne
  • A cewarsa, an samu wannan nasarar ne sakamakon yadda ‘yan sanda su ka hada kai da mafarauta da ‘Yan sa kai tare da jajircewar su

Jihar Adamawa - Rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa ta kama mutane 21 da ake zargin su na da hannu a halaka mutane 7 da tsafi a wani kauyen Adamawa, kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Aliyu Adamu, kwamishinan ‘yan sandan jihar, a wani taron manema labarai na ranar Litinin a Yola, ya tabbatar da kama mutanen wadanda ‘yan kauyen Dasun Bwate ne karkashin karamar hukumar Fufore a jihar.

Kara karanta wannan

‘Yan bindigan da aka fatattako daga Zamfara sun tare hanyoyin Katsina suna neman abinci

Adamawa: ‘Yan sanda sun kama mutum 21 da ake zargin sun halaka mutum 7 da tsafi
Taswirar Jihar Adamawa. Hoto: The Punch
Asali: UGC

‘Yan sandan sun samu nasarar ne saboda jajircewar su

A cewar Adamu, an samu wannan nasarar ne sakamakon dagewar su da hadin kai da mafarauta da ‘Yan sa kan yankin, sannan har da tsayawa tsayin-daka wurin kin amincewa da rashawa.

“Ina so in bayyana cewa jami’an rundunar ‘yan sanda sun nuna rashin amincewar su da rashawa karara.
“Rundunar ta yi bincike kuma ta kama mutane 1,146 akan laifuka daban-daban da suka aikata a fadin jihar, yanzu haka mutane 426 a cikin su sun fuskanci hukunci sannan mutane 720 su na jiran hukunci,” kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Ana zargin wadanda aka kama da hannu a kashe-kashen mutane 7

Adamu ya ce:

“Hakan ya kawo tarin nasarori, ciki har da kama mutane 21 da ake zargin su na da hannu a halaka mutane 7 a Dasin Bwate. Yanzu haka ana ci gaba da bincike an kuma kwantar da tarzomar yankin".

Kara karanta wannan

Hotunan matasa biyu da aka kama bisa yunkurin baiwa ƴan sanda cin hancin N500,000 a Legas

A cewar kwamishinan, rundunar ta samu nasarar kama wasu ‘yan daba da aka fi sani da Yaran Shilla fiye da 400, wadanda suka addabi mutanen Yola da kewaye, kuma an hukunta su yadda ya dace.

Adamawa: Jarumin mai shago ya ragargaji ‘yan daba 2 da su ka yi kokarin fasa masa shago

A wani rahoton, kun ji wani mai shago, Mohammed Hamman Adama, ya nuna gwarzontakarsa bayan ya yi dambe da wasu yaran Shila yayin da su ka yi kokarin balle masa shagon sa da ke Sangere Bode a karamar hukumar Yola ta kudu a jihar Adamawa.

LIB ta ruwaito yadda aka tattaro bayanai akan wadanda ake zargin, Umar Sa’ad, mai shekaru 18 da Mohammed Idris, mai shekaru 20 suka lallaba shagon sa da misalin karfe 2:00 na daren 2 ga watan Satumban 2021 da addunan su, gudumomi, sanduna da sauran miyagun makamai.

Bayan isar su shagon har sun fara balle kofar don su samu nasarar yasar shagon. Su na kici-kicin balle kofa mai shagon ya ji kara ya fita cikin sauri.

Asali: Legit.ng

Online view pixel