Da duminsa: Sanwo-Olu ya sa hannu kan dokar hana kiwo a fili a Legas

Da duminsa: Sanwo-Olu ya sa hannu kan dokar hana kiwo a fili a Legas

  • Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu ya rattaba hannu kan dokar hana kiwo a sarari
  • Gwamnan ya yarda da sabuwar dokar ne kamar yadda takwarorinsa na kudancin kasar nan su ka yi
  • Gwamnan ya bukaci dukkan hukumomin tsaro da su tashi tare da fada wa aikin hana kiwo a sarari a fadin jihar

Lagos - Gwamna Babajide Sanwo-Olu na jihar Legas ya sa hannu kan dokar hana kiwo a fadin jihar Legas, Daily Trust ta ruwaito.

Gwamnan ya yarda da dokar ne a ranar Litinin, hakan na nuna ya bi sahun takwarorinsa na kudancin kasar nan wadanda tun farko suka fara sa hannu kan dokar.

Da duminsa: Sanwo-Olu ya sa hannu kan dokar hana kiwo a fili a Legas
Da duminsa: Sanwo-Olu ya sa hannu kan dokar hana kiwo a fili a Legas. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Gwamnan ya saka hannu kan dokar ne bayan kwanaki 11 da 'yan majalisarsa suka amince da ita kuma suka mika masa domin mayar da ita doka.

Kara karanta wannan

Son hada kan Najeriya na saka ni hauka, Okorocha ya nuna damuwarsa kan Najeriya

Sa hannun kan dokar hana kiwon a sarari da gwamnan ya yi ta biyo bayan hukuncin da kungiyar gwamnonin kudu suka yanke a watan Augustan da ya gabata, inda suka saka watan Satumba ya zama watan karshen da mambobin za su saka hannu a kai.

Rikici daban-daban sun dinga ballewa a wasu jihohi, lamarin da yasa gwamnonin suka dinga dora laifi kan kiwo a sarari, Daily Trust ta ruwaito hakan.

Sanwo-Olu wanda ya amince da dokar kuma ya saka hannu yayin taron majalisar zartarwar jihar da aka yi a Alausa, ya umarci dukkan hukumomin tsaro da su gaggauta fada wa aiki kamar yadda tanadin dokar ya bada.

Ya ce:

"Da karfin ikon da na ke da shi a matsayin gwamnan jihar Legas, na saka hannu kan dokar hana kiwon sarari da kuma kutsen shanu a gonaki, hakan ya zama doka kuma ta haramta dukkan abinda ya hada da kiwon dabbobi a sarari."

Kara karanta wannan

Da duminsa: 'Yan bindiga na luguden wuta a kudancin Kaduna

Kaduna: Hotunan 'yan sanda masu murabus suna yi wa hukumar fansho zanga-zanga

Gwamnonin jihohin Rivers, Ondo, Enugu da Akwa Ibom tuni suka rattaba hannu kan dokar.

A wani labari na daban, 'yan sandan da suka yi murabus sun fita zanga-zangar lumana kan rike musu kudade da hukumar fansho ta jihar Kaduna ta yi a ranar Litinin, Daily Trust ta ruwaito.

Jami'an sun yi tattaki har zuwa hedkwatar rundunar 'yan sandan jihar Kaduna domin mika kokensu inda suka jaddada cewa ba su da ra'ayin abinda suka kwatanta da "hukumar kisa".

A na tsawon wani lokaci, jami'an 'yan sanda a kasar nan suna ta kushe hukumar fansho.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel