Da duminsa: 'Yan bindiga na luguden wuta a kudancin Kaduna

Da duminsa: 'Yan bindiga na luguden wuta a kudancin Kaduna

  • Gagararrun 'yan bindiga sun kai farmaki yankin Zunuruk Agban da ke Kagoro a karamar hukumar Kaura
  • Miyagun an gano sun kai farmakin ne wurin karfe 7:30 zuwa 8:00 na daren Lahadi a Kaduna
  • Sai dai, har a lokacin rubuta wannan rahoton, ba a tabbatar da mutum nawa suka sata ko raunata ba

Kaura, Kaduna - A daren Lahadi ne miyagun 'yan bindiga suka kutsa yankin Zunuruk Agban da ke yankin Kagoro a karamar hukumar Kaura ta jihar Kaduna.

Kamar yadda Daily Trust ta tattaro, miyagun sun kaddamar da farmakin wurin karfe 7:30 zuwa 8:00 na dare.

Sai dai, har a lokacin rubuta wannan rahoton, ba a san mutum nawa suka sata ko suka raunata ba.

Da duminsa: 'Yan bindiga na luguden wuta a kudancin Kaduna
Da duminsa: 'Yan bindiga na luguden wuta a kudancin Kaduna
Asali: Original

Nan da shekaru 2 za a kammala wurin kiwon shanun jihar Kaduna na N10bn, El-Rufai

Kara karanta wannan

Nan da shekaru 2 za a kammala wurin kiwon shanun jihar Kaduna na N10bn, El-Rufai

A wani labari na daban, Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna a ranar Talata, ya ce jiharsa ta fara aikin naira biliyan goma na gina wurin kiwo ga makiyaya a jihar Kaduna.

Daily Trust ta ruwaito cewa, El-Rufai, wanda ya zanta da manema labarai yayin wani taro da jami'an jam'iyyar APC a sakateriya jam'iyyyar da ke Abuja, ya ce nan da shekaru biyu za a kammala aikin.

Gwamnan ya ce babban bankin Najeriya na CBN shi ya taimaka wa jihar da kudi har N7.5 biliyan domin samun nasarar aikin, Daily Trust ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel