'Yan bindiga sun sheke rayuka 5, sun raunata wasu 5 a Kebbi

'Yan bindiga sun sheke rayuka 5, sun raunata wasu 5 a Kebbi

  • Miyagun 'yan bindiga sun kai farmaki kauyen Uchukku da ke karamar hukumar Shanga ta jihar Kebbi
  • Sun sheke mutum 5 'yan gida daya tare da raunata wasu biyar yayin satar shanun da suka je yi a gidan
  • A take mutum hudu suka mutu, daya kuwa sai da aka kai shi asibiti yayin da sauran biyar din ke jinya

Shanga, Kebbi - Miyagun 'yan bindiga sun halaka rayuka biyar tare da barin wasu biyar da miyagun raunika a karamar hukumar Shanga ta jihar Kebbi, Daily Trust ta tattaro.

'Yan bindigan sun tsinkayi kauyen Uchukku a sa'o'in farko na ranar Juma'a, sun sace shanu tare da harbe mutum 5 har lahira.

'Yan bindiga sun sheke rayuka 5, sun raunata wasu 5 a Kebbi
'Yan bindiga sun sheke rayuka 5, sun raunata wasu 5 a Kebbi. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Wani mazaunin Shanga mai suna Yushau Garba Shanga, ya sanar da Daily Trust cewa, 'yan bindigan sun kai farmaki wurin karfe 1:50 na dare.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun afkawa coci ana cikin ibada, sun kashe mutum 1, sun sace 3

Ya kara da cewa mutum hudu sun rasu a take yayin da dayan ya rasu bayan an kai shi asibiti.

Kamar yadda yace, mutanen da suka samu rauni an kwantar da su a asibitin Shanga domin samun kulawar masana.

Ya ce daga cikin wadanda suka samu raunin har da karamar yarinya wacce aka harba a kafarta.

Ya bayyana cewa, tuni jama'ar yankin da lamarin ya faru da su suka tsere tare da gudun hijira.

Ya ce:

"Mutum biyar din da aka kashe duk 'yan gida daya ne. 'Yan uwan juna ne.
"'Yan bindigan sun kai farmaki yankin wurin karfe 1:50 na daren Juma'a.
"Kai tsaye gidan suka je domin sace shanunsu kuma suka kashe mutum biyar a yayin satar."

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, DSP Nafiu Abubakar bai dauka waya da aka dinga kiran shi ba kuma bai amsa sakon kar ta kwana da aka dinga tura masa ba.

Kara karanta wannan

'Yan ta'adda sun halaka rai 1, sun yi garkuwa da wasu a Sokoto

Yobe: Jama'ar da jirgin NAF ya yi wa luguden wuta suna bukatar diyya

A wani labari na daban, iyalan wadanda mummunan lamarin da ya faru a jihar Yobe da su sakamakon luguden wutan da jirgin NAF ya so yi kan 'yan ta'addan Boko Haram, sun bukaci gwamnatin tarayya da ta biya su diyya.

Sun alakanta bukatarsu da dalilin cewa, gwamnati a kowanne mataki a Najeriya ba ta cika biyan diyya ba ga jama'a da aka yi wa barna, Daily Trust ta ruwaito.

Daga ciki mutum takwas da suka rasu, tsoffafi uku da wata mata wadanda suka bar kananan yara. Akwai yara kanana hudu da suka rasa rayukansu da kuma wasu gidaje da suka kone.

Asali: Legit.ng

Online view pixel