Yanzu-Yanzu: Tsohon mataimakin gwamnan CBN, mai sukar Buhari ya rasu

Yanzu-Yanzu: Tsohon mataimakin gwamnan CBN, mai sukar Buhari ya rasu

  • Tsohon mataimakin gwamnan CBN, Obadiah Mailafia ya rasu bayan gajeriyar rashin lafiya
  • Mailafia kasance shaharrae wajen sukar gwamnatin Buhari, kana ya taba tsayawa takarar shugaban kasa
  • Ya yi aiki a Bankin Raya Afrika (AfDB), sannan tsohon marubuci ne a jaridar Vanguard

Obadiah Mailafia, tsohon mataimakin gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), ya rasu.

Har yanzu ba a samu cikakkun bayanai game da mutuwar tasa ba, amma majiyoyi sun shaida wa Daily Trust cewa ya rasu ne bayan gajeriyar rashin lafiya.

Mailafia ya kasance mai tsananin sukar gwamnatin Buhari, ya kuma taba tsayawa takarar shugaban kasa a shekarar 2019 a karkashin jam'iyyar ADC.

Yanzu-Yanzu: Tsohon mataimakin gwamnan CBN ya riga mu gidan gaskiya
Obadia Mailafia | Hoto: vanguardngr.com
Asali: Facebook

Ya yi aiki a Bankin Raya Kasashen Afirka (AfDB) kuma ya zama mataimakin gwamnan CBN tsakanin 2005 zuwa 2007.

Kara karanta wannan

Hotunan shugaba Buhari yayin da yake hawa jirgi zuwa kasar Amurka

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Takaitaccen tarihin Mailafia

An haife shi a ranar 24 ga Disamba, 1956 a kauyen Randa, karamar hukumar Sanga ta jihar Kaduna, mahaifinsa Baba Mailafia Gambo Galadima, mai wa'azin bishara ne a Cocin Evangelical Reformed Church of Central Nigeria.

Ya fara karatunsa a makarantar Musha Sudan United Mission School daga 1964 zuwa 1969 sannan ya wuce Makarantar Sakandaren Mada Hills, Akwanga, Nasarawa, daga 1970 zuwa 1974. Daga bisani ya zarce zuwa Jami’ar Ahmadu Bello, Zariya, inda ya sami digiri na farko a fannin Tattalin arziki.

Hakazalika, ya taba kasancewa mai rubutu a jaridar Vanguard a wasu shekaru.

Duk da cewa ya yi fice a matsayin masani, Mailafia ya shahara sosai a kasar bayan ya ba fadi wata hira cewa an sanar da shi wani gwamna shi ne kwamandan Boko Haram.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sace dalilan jami'a kwanaki kadan bayan sace malamansu

Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ce ta gayyace shi amma an sake shi bayan tattaunawa ta awanni.

Shugaban EFCC ya yanki jiki ya fadi yayin da yake magana a dakin taro

A wani labarin, shugaban Hukumar Yaki da Yiwa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC), Abdulrasheed Bawa ya yanki jiki ya fadi a bikin ranar kasa ta uku a Banquet Hall Villa, Tribune Nigeria ta ruwaito.

Bawa wanda ke isar da sakon fatan alheri ba zato ba tsammani ya carke, ya koma kan kujerarsa, ya yanki jiki ya zube. Bawa ya tsaya da magana ya rufe fuskarsa da tafin hannunsa na dama, yana mai cewa:

"Don Allah, ku gafarce ni, ba zan iya ci gaba ba."

Asali: Legit.ng

Online view pixel