Tuhumar FBI: Buhari ne zai yanke hukunci kan Abba Kyari, Ministan harkokin yan sanda

Tuhumar FBI: Buhari ne zai yanke hukunci kan Abba Kyari, Ministan harkokin yan sanda

  • Rahoton binciken Abba Kyari ya dira gaban ofishin Antoni Janar
  • Daga bisani za'a mika rahoton teburin shugaba Muhammadu Buhari, cewar Minista
  • An dakatad da Abba Kyari daga hukumar yan sanda

Abuja - Ministan harkokin yan sanda, Muhammad Maigari Dingyadi, ya bayyana cewa shugaba Muhammadu Buharim zai yanke hukuncin karshe kan jami'in dan sanda, Abba Kyari.

Dingyadi ya bayyana hakan ne a hirar da yayi a shiri 'Politics Today' na tashar ChannelsTV ranar Talata.

Ya bayyana cewa za'a aika takardar binciken da aka yi wajen shugaba Buhari don rattafa hannu kan hukuncin da akayi masa.

An kammala bincike kan DCP Abba Kyari, IGP ya karbi rahoton

Shugaban kwamitin da Sifeto Janar na yan sanda ya nada don binciken, DIG Joseph Egbunike. ya gabatar da kundin sakamakon binciken ga IGP Mohammed Alkali a ranar Alhamis, 26 ga Agusta, 2021.

Kara karanta wannan

Mun yi ta yi wa Buhari addu’o'i amma ba mu ga sakamako ba, inji Sheikh Khalid

A jawabin, DIG Egbunike ya godewa IGP bisa yarda da kwamitinsa da mambobinta da wannan aiki na bincike mai muhimmanci.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Bayan gabatar da rahoton, IGP Alkali ya godewa kwamitin bisa aikin da sukayi kuma yayi alkawarin cewa za'a duba rahoton kuma za'a dauki matakin da ya kamata.

Buhari ne zai yanke hukunci kan Abba Kyari, Ministan harkokin yan sanda
Tuhumar FBI: Buhari ne zai yanke hukunci kan Abba Kyari, Ministan harkokin yan sanda Hoto: Hushpuppi/Abba Kyari
Asali: Facebook

Zamu bi hanyar da ya dace

Ministan ya bayyana cewa yan sanda zasu bi hanyar da ta dace akan lamarin Abba Kyari.

Yace, za'a nemi shawarwari na shari'a daga ofishin Babban lauya kafin a yanke hukuncin

Ya kara da cewa yana da matukar muhimmanci bisa la'akari da lamarin ya shafi kasashe biyu, harma da ministan harkokin kasashen waje.

Yace,:

"Lamarin Abba Kyari ya bazu ko ina kuma ina tunanin mutane yanzu sunji cewa bisa jajircewa da neman adalci, yan sanda sun kafa kwamitin da zasu binciki dukkanin wannan kazafin.

Kara karanta wannan

Jerin fitattun 'yan Najeriya 4 da Buhari zai iya nadawa a matsayin sabon ministan noma

Mun bayyana cewa kwamitin sun mika rahoton binciken ga IGP. Mun kuma mika rahoton ga Babban lauyan kasar domin a duba a shari'ance sannan daga bisani zamu mika ga Shugaban kasa domin yanke hukuncin karshe.
Zaka iya lura cewa ko da yake lamarin na cikin gida ne amma ya dan kunshi Kasar waje. Yana da muhimmanci muyi abinda ya dace. Muna bukatar mu tuntubi ma'aikatar harkokin kasashen waje da ma'aikatar Shari'a kafin a yanke hukuncin karshe."

Me ya faru da DCP Abba Kyari?

FBI ta yi zargin Abass Ramon wanda aka fi sani da Hushpuppi, ya bai wa Abba Kyari N8m ko $20,600, don kamawa da tsare wani abokin harkallarsa mai suna Kelly Vincent.

Legit.ng ta tattaro cewa batun na cikin takardar da Kotun Amurka ta bayar na gundumar tsakiyar California mai dauke da kwanan wata 12 ga Fabrairu, 2021.

Takardar ta yi zargin cewa Hushpuppi ya ba Kyari kwangila bayan da Chibuzo ya yi barazanar fallasa wani zamba na dala miliyan 1.1 da suka aikata a kan wani dan kasuwa na kasar Qatar.

Kara karanta wannan

Buhari: Gwamnan Ebonyi ya yi wa Wike raddi, ya fallasa wadanda suka kawo matsalar tsaro

A cewar rahoton, shafi na 59, sakin layi na 145 na takardar ya bayyana cewa Kyari ya bayar da bayanan asusu na wani asusun bankin Najeriya mai dauke da sunan da ba nashi ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel