Yan Boko Haram sun fara komawa Kaduna daga Sambisa, Hukumar DSS

Yan Boko Haram sun fara komawa Kaduna daga Sambisa, Hukumar DSS

  • DSS ta bankado yadda yan Boko Haram ke komawa jihar Kaduna
  • An ankarar da jami'an tsaro su mike tsaye tun da wuri kan abu yayi tsauri
  • Fiye da shekaru 10 kenan Najeriya na fama da rikicin yan ta'addan Boko Haram

Hukumar DSS tace yan Boko Haram sun fara guduwa daga dajin Sambisa dake jihar Borno zuwa karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna.

A cewar Punch, an samu wannan labari ne a takarda mai take, 'Karin bayani na komawaryan ta'adan Boko Haram zuwa Rijana a jihar Kaduna.' tare da sa hannun DCG B.O Bassey, mataimakin kwamandan bincike na hukumar NSCDC.

A cewar takardar, wasu manyan yan Boko Haram na shirin hada kai da wani Adamu Yunusa da mabiyansa.

Kara karanta wannan

Jerin sunaye: Manyan 'yan siyasa 5 da aka kayar a 2019 wadanda ka iya dawowa da karfi a shekarar 2023

Saboda haka hukumar DSS ke ankarar da jami'an tsaro su farga.

A cewar takardar:

"An gano shirin wani babban dan Boko Haram, Ibrahim (FNU) tare da yaransa suna tashi daga dajin Sambisa a Borno zuwa dajin Rijana a karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna domin hada kai da wani Adamu Yunusu (Saddiqu)."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Saboda haka, ana kira gareku su tashi tsaye wajen sintiri da binciken leken asiri kan wadannan wurare."

An hallaka Shugaban yan ta'addan ISWAP, AlBarnawy

Bayan shekaru da dama ana farautarsa, an samu nasarar hallaka shugaban yan ta'addan ISWAP Mus'ab Albarnawy a jihar Borno, rahoton DailyTrust.

An samu rahoton cewa an kashe Albarnawy ne a karshen watan Agustan 2021.

Mus'ab Al-Barnawi ne 'dan mu'asassin Boko Haram, Mohammed Yusuf, wanda shine jami'an tsaro suka kashe a 2009 yayinda yayi fito-na-fito da gwamnati.

Kara karanta wannan

Ina tabbatar muku za'a hukunta tubabbun yan Boko Haram: Kwamandan Operation Hadin kai

An samu riwayoyi biyu game da labarin mutuwarsa. Yayinda riwayar farko tace Sojojin Najeriya ne suka hallakashi, wata riwayar tace rikicin cikin gida tsakaninsa da sauran yan ta'addan ISWAP yayi sanadiyar mutuwarsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel