Yadda ‘Yan Sanda suka kama ‘Dan bindigan da ke da hannu wajen sace 'Yan makaranta a Kaduna
- ‘Yan Sanda sun damke wani wanda ya yi fice wajen garkuwa da mutane a Kaduna
- Usman Mohammed mutumin Zamfara ne wanda yake satar mutane a Igabi da Giwa
- ‘Dan bindigan ya taimaka wajen wasu sace-sacen dalibai da aka rika yi a makarantu
Kaduna - A ranar Alhamis, 17 ga watan Satumba, 2021, jami’an ‘yan sandan jihar Kaduna suka ce sun kama wani da ake zargi da hannu a satar yaran makaranta.
Punch tace ‘yan sanda suna kyautata zaton wannan mutum ya taimaka wajen dauke daliban makaranar Bethel Baptist High School, da na jami’ar Greenfield.
Mai magana da yawun bakin ‘yan sandan Kaduna, Mohammed Jalige, ya gabatar da wannan mutumi da ake tuhuma da laifi a babban ofishin ‘yan sandan jihar.
Dubu ta cika
Rahoton yace haka zalika wadanda ake zargi da dauke dalibai 37 har da wata mai dauke da juna biyu daga makarantar gwandu a Afaka, Igabi suna hannun hukuma.
Har ila yau, Mohammed Jalige, ya gabatar wa Duniya wadanda ake zargi da kashe Abdulkareem Na’Allah har gida. Su ma dai tuni duk suka amsa laifinsu da kansu.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
An kama Usman Mohammed
Jalige yace wani Usman Mohammed daga Bukuyum a jihar Zamfara ya shiga hannunsu bisa zarginsa da hannu wajen daukar daliban wadannan makarantu uku.
Usman Mohammed yana cikin wadanda suka addabi garuruwan Kaduna da Giwa da satar mutane.
Kamar yadda muka samu labari, Mohammed mai shekara 41 ya amsa laifinsa bayan ya shiga hannun jami’an tsaro, yace ya saba tsare mutane har sai an biya kudi.
“Bayan samun bayanan sirri a ranar 29 ga watan Agusta, 2021 da kimanin karfe 9:00, dakarun Operation Yaki da tawagar FIB STS daga Abuja suka kutsa wani gida a Asikolaye, Kaduna inda aka damke wani Usman Abubakar (namiji mai shekara 41), ‘dan asalin kauyen Adakpa, Bukkuyum, jihar Zamfara, wani gawurtaccen ‘dan bindigan da ya addabi Chikun, Igabi, da Giwa a jihar Kaduna.”
“Ya amsa laifin garkuwa da mutane da dama yana karbar kudin fansa; yana kuma da hannu a harin da aka kai a jami’ar Greenfield, Bethel Baptist Academy da makarantar gwandu a Mando, Kaduna.”
IGP ya kai ziyara a Kwara
A jiya an ji Kwamishinan ‘Yan Sanda na jihar Kwara ya kai kuka wajen IGP. inda ya shaida masa cewa babu isasshen kayan aiki, sannan jami'ai sun yi masu kadan.
Usman Alkali Baba ya yi albashir a garin Ilorin, ya shaida wa kwamishinan cewa rundunar ‘Yan Sanda za ta kara yawan jami’ai da mutum 20, 000 a shekaru biyu.
Asali: Legit.ng