Da duminsa: 'Yan sanda sun yi ram da makasan dan Sanata Na'Allah

Da duminsa: 'Yan sanda sun yi ram da makasan dan Sanata Na'Allah

  • An kama wasu mutane 2 da ake zargin su na da masaniya a kan kisan Abdulkareem Na’Allah
  • Abdulkareem da ne ga Sanata Bala Ibn Na’Allah kuma an kama su a kwanaki kadan da suka gabata
  • Bayan kama matasan guda biyu masu shekaru ashirin da doriya, an tsinci motar mamacin a kusa da Nijar

Kaduna - An kama wasu mutane 2 da ake zargin su na da masaniya a kan kisan Abdulkareem Na’Allah, dan Sanata Bala Ibn Na’Allah mai shekaru 36.

Daily Trust ta ruwaito cewa, kamar yadda rahotanni suka bayyana, kwanaki kadan da suka gabata kenan da kama su.

Da duminsa: 'Yan bindiga sun yi ram da makasan dan Sanata Na'Allah
Da duminsa: 'Yan bindiga sun yi ram da makasan dan Sanata Na'Allah. Hoto daga Daily Trust
Asali: UGC

A ranar 29 ga watan Augustan 2021 aka tsinci gawar Abdulkareem, babban dan sanatan a dakin sa da ke Malali GRA a Kaduna.

Sai dai babu kwararan bayanai a kan wadanda aka kama amma dai shekarun su 20 da ‘yan kai da haihuwa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An tsinci abin hawan mamacin a wuraren iyakar Nijar.

Daily Trust ta tabbatar da kamen har ta tuntubi Kakakin rundunar ‘yan sandan yankin, ASP Jalige Mohammed.

“Tabbas akwai wasu mutane 2 da ake zargin su ne makasan Abdulkareem Na’Allah,” a cewar sa.

Mahaifin mamacin shine sanata mai wakiltar mazabar Kebbi ta kudu.

IGP ya nada sabuwar mai magana da yawun rundunar 'yan sandan FCT

A wani labari na daban, Sifeta janar na ‘yan sanda, Usman Baba ya amince da nadin DSP Josephine Adeh a matsayin jami’ar hulda da jama’an rundunar ‘yan sanda na babban birnin tarayya, Abuja.

Daily Nigerian ta ruwaito cewa, a wata takarda wacce ya saki a ranar Talata a Abuja, ya ce sabuwar jami’ar hulda da jama’ar za ta fara aiki ne take-yanke.

Adeh ta maye gurbin ASP Daniel Ndirpaya ne wanda yanzu aka yi wa karin girma zuwa kwamishinan ‘yan sanda na Abuja a ranar 31 ga watan Augusta.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel