IGP: Buhari ya sharewa ‘Yan sanda hawaye, za mu dauki jami’ai 20, 000 aiki a shekarar bana

IGP: Buhari ya sharewa ‘Yan sanda hawaye, za mu dauki jami’ai 20, 000 aiki a shekarar bana

  • Sufeta-Janar na ‘yan sanda, Usman Alkali Baba ya ziyarci Jihar Kwara
  • Kwamishinan ‘Yan sanda ya kawo kukan rashin isassun jami’ai a Jihar
  • IGP Usman Baba yace yawan ‘yan sanda zai karu da 20, 000 nan da 2022

Kwara - Sufeta-Janar na ‘yan sandan Najeriya, ya bayyana cewa rundunar jami’an tsaron za ta dauki jami’ai 20, 000 aiki daga yanzu zuwa shekarar 2020.

Jaridar The Nation tace Usman Alkali Baba ya yi wannan bayani ne a lokacin da ya kai ziyara ta musamman zuwa ofishin ‘yan sanda da ke Ilorin, jihar Kwara.

IGP Usman Alkali Baba yace shugaban kasa ya ba su damar daukar jami’ai 10, 000 a kowace shekara, yace a shekarar nan ba a dauki sababbin jami’an ba.

Jawabin IGP a Jihar Kwara

“Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince mu dauki mutum 10, 000 aiki duk shekara har na tsawon shekaru shida.”

Kara karanta wannan

Yadda dakile layin wayoyin GSM ya jawo ‘Yan bindiga suka kai wa Sojoji hari a Zamfara

“Mun fara yin wannan, amma a shekarar 2020 ba mu yi ba.”
“Saboda haka daga yanzu zuwa karshen shekara za mu dauki na 2020 da na 2021. Za ayi watanni shida ana horas da su.”

IGP Usman Alkali Baba
Usman Alkali Baba da Yemi Osinbajo Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

"Zuwa karshen shekarar nan, adadin jami’an ‘yan sanda zai kara yawa da mutane 20, 000 a shekarar 2020.”

A game da yaki da ‘yan bindiga, shugaban dakarun ‘yan sandan yace sojoji da sauran jami’an tsaro na gaba wajen wannan kokari, kuma ana samun nasara.

CP Emienbo Assayomo ya kawo kuka

Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Kwara, Emienbo Assayomo a na shi jawabin, yace suna fama da karancin dakaru, ‘yan sanda 3, 500 kadai ake da su a Kwara.

“An kafa rundunar jihar Kwara da ‘yan sanda 8, 000, amma yau dakarunmu ba su kai 3, 500 ba. A halin yanzu haka ba mu da makaman APC masu lafiya.”

Kara karanta wannan

Hotunan ‘Pre-wedding’ din Jaruma Adamar Kamaye da wani Matashi suna yawo

Rahoton yace duk da jihar tayi fadi har zuwa yankin Kaiama da Baruten inda ta yi iyaka da Neja, CP Assayomo yace babu kayan aiki da za a tunkari 'yan fasa kauri.

Yaki da 'yan bindiga a Zamfara

A farkon makon nan aka ji Gwamnan Zamfara, Bello Matawalle yana bayanin nasarorin da aka samu a dalilin dakile layin GSM saboda a kawo karshen 'yan bindiga.

Toshe layukan waya ya sa ‘Yan bindiga sun koma yi wa wadanda suka dauke bulala domin sun rasa kudin fansa, sannan ana ta kama masu ba 'yan bindiga bayanai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel