Asiri ya tonu: Mun cafke mutum fiye da 100 da ke ba ‘Yan bindiga bayanai a Zamfara inji Matawalle

Asiri ya tonu: Mun cafke mutum fiye da 100 da ke ba ‘Yan bindiga bayanai a Zamfara inji Matawalle

  • Wasu daga cikin masu ba ‘Yan bindiga bayanai sun fada hannun hukuma
  • Gwamna Bello Matawalle yace an ci nasara ne bayan toshe layukan waya
  • Matawalle ya yi bayanin yadda aka ceto daliban da aka dauke a Muradun

Zamfara - Gwamnatin jihar Zamfara tace ta damke wasu mutane sama da 100 da ake zargin suna taimaka wa miyagun ‘yan bindiga da ke ta’adi da bayanai.

Mai girma gwamna Bello Muhammad Matawalle ya bayyana haka a lokacin da BBC Hausa ta yi wata hira ta musamman da shi a gidansa da ke garin Gusau.

Bello Muhammad Matawalle yace an samu wannan nasara ne bayan an kashe layukan waya a jihar.

Legit.ng Hausa tana da labari cewa wadannan masu ba ‘yan bindiga bayanai, sune suke jawo su cikin al’umma, suna fada masu sirrin wadanda za su dauka.

Kara karanta wannan

An bankado sabbin mafakar ‘yan bindigar Zamfara da ke tserewa

'Yan bindiga sun rasa kudin fansa

"Toshe duk wata hanyar sadarwa tsakanin masu kwarmata bayanai ga ƴan bindiga ya yi tasiri sosai domin yanzu mun kama 'infoma' fiye da 100."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Gwamna Matawalle ya shaida wa BBC cewa a sakamakon dakile hanyoyin sadarwa da aka yi kwanaki, ‘yan bindigan ba su samun damar karbar kudin fansa.

Matawalle
Gwamnan Zamfara, Bello Matawalle Hoto: globaltimes.com
Asali: UGC

"Babu wani babban abin da ya faru. ƴan bindiga sun koma suna yi wa wadanda suka sace bulala a madadin kuɗin fansa da suka rasa."

An ceto ɗaliban makaranta

Rahoton yace Gwamnan na Zamfara ya yi magana game da kubuto dalibai sama da 70 da aka yi daga hannun ‘yan bindiga a mahaifarsa, garin Kayar Muradun.

Bello Matawalle yake cewa tubabbun ‘yan bindiga aka yi amfani da su, aka kubutar da wadannan yara.

Kara karanta wannan

Ba zan sake afuwa gare ku ba, gwamnan arewa ga ‘yan bindiga, ya sha alwashin hukunta masu daukar nauyinsu

Gwamnan yace bayan tsinke layukan ne wani tubabban ‘dan bindiga yayi alkawarin zai gano inda yaran suke, ana samun labari kuwa, aka tura sojoji suka ceto su.

Binciken hadarin da ya kashe COAS

NAF ta karbi bayanai a kan binciken da aka gabatar game da mummunan hadarin jirgin saman da ya kashe tsohon hafsun sojojin kasa, Janar Attahiru Ibrahim.

Sai bayan kwanaki 117 da mutuwar Hafsun sojojin aka karkare binciken hadarin da ya auku a Kaduna. Sai a ranar Larabar nan ne rahoton ya je hannun sojoji.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng