Hotunan matasa biyu da aka kama bisa yunkurin baiwa ƴan sanda cin hancin N500,000 a Legas
- Rundunar ‘yan sandan jihar Legas sun kama wasu matasa 2 bisa yunkurin ba su cin hancin N500,000 don amshi ‘yan ta’adda daga hannun su
- A wata takarda wacce kakakin rundunar na jihar, Adekunle Ajisebutu ya saki ya bayyana cewa sun bayar ne don a saki wasu
- Sai dai ‘yan sandan sun nuna nagartar su ta hanyar kin amsar kudin kuma suka kama su don su fuskanci hukunci
Jihar Legas - Rundunar ‘yan sandan jihar Legas ta kama wasu matasa 2 sakamakon yunkurin ba wa jami’an ta rashawa don su saki wasu da ake zargin ‘yan ta’adda ne su kubutar dasu daga hukunci.
A wata takarda wacce LIB ta ruwaito yadda kakakin rundunar, Adekunle Ajisebutu ya ce wani Adariku Sunday mai shekaru 34, mazaunin gida mai lamba ta 66 da ke Henry Smith Close Abidjan GRA, Ajah ya bai wa ‘Yan sanda N400,000 a matsayin rashawa don su saki wani da ake zargin sa da fashi da makamai.
Sannan wani Folorunso Akeem mai shekaru 43 ya basu N100,000 don su saki wani da ake zargin dan kungiyar asiri ne.
Kakakin rundunar ya ce ‘yan sandan sun ki amsar rashawar
Dangane da batun wadanda suka so su kubutar, Ajisebutu ya ce:
“Rundunar ‘yan sanda ta sintiri a bangaren Area J, Elemoro ta kama wani da ake zargin dan fashi ne da kuma wani da ake zargin dan kungiyar asiri ne da wata bindigar toka.”
Ya kara da cewa:
“An kama Alabi Timothy mai shekaru 23 mazaunin gida mai lamba 9 kan layin Baale, Majek, Ajah da misalin karfe 12:30 na daren ranar 4 ga watan Satumban 2021 a General Paint, Garden Area a Lekki yayin da ‘yan sanda suke sintiri.”
Daya daga cikin wadanda aka so kubutarwa ya adana bindigar tokar da harsasai a cikin wata jakar sa
An kama shi da bindigar toka da kuma harsasai wadanda ya adana a wata jaka.
LIB ta ruwaito ya ce:
“Sannan sun kama wani Badmus Toheed mai shekaru 22 kuma ya bayyana cewa shi dan kungiyar asiri ne daga anguwar Aye yake, da harsasai a Ajah da misalin karfe 12:45 na daren ranar 4 ga watan Satumban 2021.”
Hotunan mutumin da aka kama ya damfari mutane 64 miliyoyin naira a Kano
A wani rahoton daban, Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta kama wani hatsabibin dan damfara bisa zargin sa da amfani da sunan babban bankin Najeriya wurin yasar dukiyar mutane 64 ta hanyar amfani da takardun bogi, LIB ta ruwaito.
Kakakin rundunar, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana hakan a wata takarda ta ranar Laraba, 8 ga watan Satumba inda yace an kama wanda ake zargin, Buhari Hassan a Yankaba Quarters ne da ke jihar.
Asali: Legit.ng