Hotunan tsohon soja mai shekaru 60 da wani da aka kama da wiwi N7.5m maƙare a mota a Kaduna

Hotunan tsohon soja mai shekaru 60 da wani da aka kama da wiwi N7.5m maƙare a mota a Kaduna

  • Dakarun sojojin na OPSH sun kama wasu masu safarar miyagun kwayoyi a hanyar Jos dauke da wiwi na N7.5m
  • Wadanda aka kama sun kunshi wani tsohon soja mai shekaru 60 da wani mutum mai shekaru 50
  • Sojojin sun mika wadanda ake zargin hannun hukumar yaki da safara da shan miyagun kwayoyi NDLEA

Kaduna - Dakarun Safe Haven (OPSH), a ranar Talara, 14 ga watan Satumba sun yi nasarar kama wasu masu safarar miyagun kwayoyi sun kwato wasu ganye da ake zargin wiwi ne da aka kiyasta kudinsa ya kai N7.5m a Kaduna, rahoton LIB.

Mai magana da yawun rundunar, Manjo Ishaku Takwa ya ce an boye abin ne cikin wata mota kirar Toyoya Camry mai lamban Legas, KJA 150 EG.

Kara karanta wannan

An Cafke Hatsabibin Ɓarawon Shanu Da Mai Safarar Miyagun Ƙwayoyi a Jihar Katsina

Hotunan tsohon soja mai shekaru 60 da wani da aka kama da wiwi na N7.5m a Kaduna
Hotunan tsohon soja da wani mutum da aka kama da muggan kwayoyi a hanyar Kaduna. Hoto: LIB
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Hotunan tsohon soja mai shekaru 60 da wani da aka kama da wiwi na N7.5m a Kaduna
Hotunan kwayoyin da aka kama hannun wani tsohon soja a hanyan Kaduna. Hoto: LIB
Asali: Facebook

Takwa ya ce:

"Wadanda ake zargin, tsohon kofur Essien Friday, tsohon soja mai shekaru 60 da wani Ibrahim Ali mai shekaru 50, yayin da dakarun ke tare motocci suna bincike a kan hanyar Manchock zuwa Jos a karamar hukumar Kaura a jihar Kaduna."

Wadanda ake zargin sun yi ikirarin an dauke su kwangila ne su kai haramtaccen abin Yola, Jihar Adamawa daga jihar Ondo kamar yadda LIB ta ruwaito.

Sauran abubuwan da aka kwace daga hannunsu sun kunshi, ganyen wiwii 18 da aka nada, wayoyin salula 2, jakunan tafiya 3, lita daya da jakunan kudin maza dauke da N570.

Tuni dai an mika wadanda ake zargin a hannun hukumar yaki da safara da ta'amullin miyagun kwayoyi NDLEA reshen jihar Plateau.

Kwamandan OPSH ya jinjinawa dakarunsa

Kara karanta wannan

Jirgin yaki ya yi luguden wuta kan al’umman gari? Rundunar soji ta yi martani kan rahoton

Hotunan tsohon soja mai shekaru 60 da wani da aka kama da wiwi na N7.5m a Kaduna
Shugaban rundunar OPSH na mika wadanda ake zargin hannun NDLEA reshen jihar Plateau. Hoto: LIB
Asali: Facebook

Hotunan tsohon soja mai shekaru 60 da wani da aka kama da wiwi na N7.5m a Kaduna
Hotunan muggan kwayoyi da aka kama a hannun tsohon soja da wani mutum hanyar Kaduna. Hoto: LIB
Asali: Facebook

Kwamandan OPSH, Manjo Janar Ibrahim Ali ya yabawa dakarun bisa jajirewarsu wurin takawa bata gari birki. Ya ce ba za su yi kasa a gwiwa ba wurin ganin sun samar da tsaro.

Ya ce OPSH za ta cigaba da hadin gwiwa da mutanen kirki masu bin doka domin kawar da laifuka yana mai kira ga mutane su rika taimaka musu da bayannai masu amfani.

Hotunan mutumin da aka kama ya damfari mutane 64 miliyoyin naira a Kano

A wani rahoton daban, Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta kama wani hatsabibin dan damfara bisa zargin sa da amfani da sunan babban bankin Najeriya wurin yasar dukiyar mutane 64 ta hanyar amfani da takardun bogi, LIB ta ruwaito.

Kakakin rundunar, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana hakan a wata takarda ta ranar Laraba, 8 ga watan Satumba inda yace an kama wanda ake zargin, Buhari Hassan a Yankaba Quarters ne da ke jihar.

Kara karanta wannan

Sojoji sun damke tsohon soja yana jigilar tulin wiwi da kwayoyi daga Ondo zuwa Jihohin Arewa

Asali: Legit.ng

Online view pixel